Kannywood
Rarara Ya Raba Tallafin Kayan Abinci Da Kudi Miliyan 75 Ga Mutane Dubu 15 A Jihar Katsina
Advertisment
Shahararren mawaƙin siyasa Dauda Kahutu Rarara, ya raba wa al’umma sama da mutum dubu 15 tallafin kayan abinci da ƙuɗaɗen cefane albarkacin azumin watan Ramadan, a mahaifarsa garin Kahutu dake ƙaramar hukumar Danja, a jihar Katsina.
Dauda kahutu Rarara ya ware Naira miliyan 75 inda ya baiwa mutum da ya amfana da tallafin Naira dubu biyar-biyar kuɗin cefane, kamar yadda mataimaki na musamman kan kafufin yada labarai Rabiu Garba gaya na fitar cewa.
Rarara ya saba irin wannan abun Wannan shi ne karo na biyu da mawaƙin ya raba tallafin kayan abinci da ƙuɗaɗe ga mutanen yankinsa a cikin watan Azumin Ramadan.
Advertisment