Rainin hankali ne dan fim ya ce yana gyaran tarbiyya ko wa’azi – Kyauta Dillaliya
Kyauta dillaliya a cikin shirin mu tattauna da gidan rediyo freedom radio kano sukeyi da jarumai da ma yan siyasa sun samu bakun cikin jaruma fati nayo wadda ankafi sa ni da kyauta dillaliya ta shirin dadin kowa.
A cikin wannan firar tayi zan tuka da dama wanda har a ciki mai tambaya yayi mata tambaya kamar haka.
Akwai wasu daga cikin ku jarumai suke cewa sun zo nemin kudi ne wasu kuma wa’azantarwa shin ke me kika zo yi ?
“Wallahi duk wanda yace maka wa’azantarwa yake karya ne yaudara kansa yayi, yanzu ga malaman sunnah dana dariƙa da yan tijjaniyya suna Allah yace annabi yace suja hadisi sai kai dan fim dan rainin hankali,yanzu haka wa’azantarwa nayi.
Yanzu na sanya gashi na sanya janbaki na sanya foda wa zaiyi wa’azantarwa nawa- inji kyauta dillaliya.
Ance kuna gyara tarbiyya?
“Kasan muna da wata al’ada idan mutum ya fadi kaza sai ka fadi kaza ni bana wa’azantarwa nishadantarwa nake a kalle ni ayi dariya shikenan ina wasa -inji kyauta dillaliya