Matasa sun daka wawa a rumbunan ajiyar abinci tare da kwashe buhuhuna a Kebbi
Wasu mazauna jihar Kebbi sun kai hari a wasu rumbunan ajiyar abinci na gwamnati da ke unguwar Bayan Kara a Birnin Kebbi, babban birnin jihar a daren ranar Asabar tare da kwashe kayan abinci.
Matasan, waɗan da suka bijirewa jami’an tsaro da ke wurin ajiyar kayan, sun kuma fasa wasu shaguna na masu zaman kansu da ke yankin, inda suka yi awon gaba da kayan abinci.
Hakazalika sun yi awon gaba da kayan abinci da wata babbar mota ta dauko, wanda ake shirin rabawa al’umma a Birnin Kebbi.
Daily Trust ta rawaito cewa da ya ke magana a kan lamarin, babban sakataren yada labarai na gwamnan jihar, Ahmed Idris, ya bayyana lamarin a matsayin “abin takaici”.
Ya ci gaba da cewa: “Tun da fari ɓatagarin sun kai hari kan kayan abinci da Dangote ya kawo jihar domin rabawa jama’a kafin su je ma’ajiyar gwamnati su kwashe.
“Irin wannan lamari bai taba faruwa a Kebbi ba. Kayayyakin abincin da suka wawashe na daga cikin kayan abincin da gwamnatin jihar ta sayo domin rabawa ga al’ummar jihar.
Jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan jihar, Nafiu Abubakar, bai amsa kiran wayar da wakilin Daily Trust ya yi masa don jin ta bakin rundunar ba.
A kwanan nan, an kai hare-hare kan rumfunan ajiya a babban birnin tarayya Abuja da Suleja a jihar Neja.
– Daily Nigerian Hausa