Mata ta kai ƙarar mijinta kotu ya sake ta dalilin hadarin mota
Rashin zaman da alkalin kotun Shari’a Musulunci ta daya ta Magajin Gari da ke a Karamar Hukumar Kaduna ta Arewa, domin ci gaba da sauraron karar da wata mata mai suna Khadijah Aliyu Nalado ta shigar da mijinta mai suna Malam Jamilu, a kan takaddamar saki ya janyo tsaiko ga shari’ar da ake yi mai dauke da lambar kara ta 4861023.
A zaman da Kotun ta yi a watan Fabirairun 2024, mai karar Khadijah, ta shigar da karar mijinta Jamilu ne, inda ta bukaci kotun ta raba aurenta na shekara uku da suka yi.
A wannan zaman na Fabirairun 2024, Jamilu ya shaida wa kotun cewa, kawai zai amince da bukatar Khadija ne idan ta biya shi Naira miliyan bakwai a matsayin ‘ Khul’i’.
Haka zalika, ya shaida wa kotun cewa, a cikin sama da shekaru biyu ya kashe Naira miliyan 2.5 a kan karatunta na Boko, tare da kuma akwatunan da ya saya mata shake da tufafi, inda kudin da ya kashe a kansu suka kai Naira miliyan 2.5, kari da wasu kudaden da ya kashe na al’adar yin aure.
Bugu da kari, ya kuma shaida wa kotun cewa, Khadijah wadda ya auro ta a Kofar Kibo a Garin Zariya, don Allah ya jarrabe shi da yin wani mummunar hatsari da motarsa, sai ta guje shi, bisa tunaninta cewa, ba zai warke daga raunukan da ya samu a lolacin hatsarin ba.
Ya kara da cewa, ta kuma yi ikirarin cewa, za ta biya ni ko nawa na kashe don in sake ta.
Sai dai, Khadija ta bakin lauyan da ya tsaya mata, Awwal Imam ya shaida wa kotun cewa, abin da za ta biya kawai shi ne Naira 100,000 kacal a matsayin sadakin da Jamilu ya bayar na aure.
Bayan wancan dage zaman kotun Jamilu ya yanke hukuncin sakinta ba tare da sai ta biya Naira miliyan bakwai da ya bukata a baya ba.
Jim kadan bayan rashin zaman Kotun, a hirarsa da LEADERSHIP Hausa a harabar Kotun Jamilu ya ce, tun bayan saki dayan da ya yi wa Khadijah ya bukaci ta kwashe kayanta daga gidansa amma ta ki.
Shi ma lauyan da ke tsaya wa Khadijah Awwal Imam ya ce, rashin zaman da kotun ba ta yi ba ne ya janyo ba a ci gaba da sauraron karar ba, amma muna fatan kafin lokacin da kotun za ta yi wani zaman, za a yi masalaha a bayan fagen kotun kan wannan takardamar.
Leadershiphausa