Kannywood

Lafiyata ƙalau babu abin da ya same ni,tura ce takai bango – Adam a zango

Adam a zango ya shiga wata damuwa da yake nunawa cewa idan ya daina fim ko waka yana ganin shi zai sanya ya samu kwanciyar hankali, saboda a yan kwanakin nan jarumin ya kama bidiyo tare da rubuce rubuce a shafinsa na sada zumunta.

Wanda har ya takai yake fadin sunayen wasu mawaka da jarumai da ya taimaka amma sunka juya masa baya amma an samu daya daga ciki ali jita ya fito ya shedawa duniya cewa tabbas ta taimakesa kuma yana bai bashi hakuri.

Wasu nagin damuwar da yake ciki itace ta sanya yake irin wanann maganganu to adam a zango yayi martani ga masu fadin haka a cikin wani gajeren bidiyo in da yake cewa.

“Bayan sallama irin ta addinin musulunci ina godiya ga duk wadanda sunka tayani da addu’a da waɗanda sunka bashi Shawara Allah ya saka da alkhairi , amma dai lafiya ta ƙalau babu abinda ya same ni , inaga ganin wasu fustin ne kamar na zare ne ko inason in kashe kai na ne akan “depression” a’a lafiya ta ƙalau nasan abinda nake yi tura ce takai bango.

In an zauna lafiya shikenan bani da matsala, tana yiyuwa ana aikomin da makamai ba wanda zai kakaɓemin ni kuma in kasa karewa ayi hakuri lafiya ta ƙalau ba abinda ya same ni, nagode sosai da shawarwari da wadanda sunka kira sukamin magana nagode – inji a zango

Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button