Labarai
Hotunan Makarantar firamare mafi Tsada A Najeriya, Ana biyan Naira Milyan 42m a matsayin ku’din makaranta a shekara
Charterhouse Dake Jihar Legas, sabuwar makarantar firamare da aka kaddamar a Lekki tare da karatun sakandarenta wanda ke karbar N42m a matsayin kudade a shekara.
Charterhouse Legas ita ce makaranta ta farko ta Burtaniya mai zaman kanta a Afirka ta Yamma kuma wani bangare ne na tsagin manyan makarantun Charterhouse.
Ga hotunan cikin makarantar da za ta fara aiki a watan Satumba.