Labarai

Gwamnatin Tinubu ta naɗa kwamitin shirya bikin cika shekara ɗaya kan mulki

Kusan shekara ɗaya bayan hawa mulkin Shugaba Bola Tinubu, Gwamnatin Tarayya ta kafa kwamitin mutum 28 domin su shirya shagulgulan cikar mulkin Tinubu shekara ɗaya.

An ɗora wa kwamitin alhakin tsara yadda za a gudanar da shagulgulan cikar mulkin Tinubu shekara ɗaya, mulkin da tun a ranar da aka rantsar da shi ya jefa ‘yan Najeriya cikin masifar tsadar rayuwa, inda ya cire tallafin fetur.

Sakataren Gwamnatin Tarayya, George Akume ne kafa kwamitin, kuma ya rantsar da ai a ofishin sa, a ranar Juma’a, kuma ya bayyana masu cewa dalilin hakan shi ne domin a bayyana wa ‘yan Najeriya irin ci gaban da wannan gwamnati ta samar da kuma tabbacin ganin an cimma shirin Fata Nagari Lamiri da gwamnatin Tinubu ta sa gaba akai.

Za a fara da taron manema labarai a ranar 22 ga Mayu, 2024.

Ranar 25 ga Satumba zuwa ranar 27 kuma ranaku ne wasu hidimomi da Uwargidan Shugaban Ƙasa za ta gudanar.

A ranar 27 ɗin ce kuma za a tattauna batutuwan da suka shafi ƙasa.

Ranar 28 ga Mayu Tinubu zai kuma Tinubu zai ƙaddamar da Gidauniyar Bunƙasa Ayyukan Fata Nagari Lamiri sai kuma ranar Talata ɗin dai za ya gana da manema labarai, wato 28 ga Mayu, 2024.

Ranar 29 ga Mayu kuma zai yi wa ‘yan Najeriya jawabi kuma yi fareti da filin faretin Abuja.

A wannan ce kuma za a yi dabdalar liyafar abinci a Fadar Shugaban Ƙasa.

Kwamitoci 11 Da Aka Kafa:

Akwai Kwamitin Addu’o’i a Coci, Kwamitin Addu’o’i a Masallaci, Kwamitin ‘Yan Kai-kawo, Kwamitin Kaɗe-kaɗe da Raye-raye, Kwamitin Kula da Lafiya, Kwamitin Tsaro, Kwamitin Jaridu da Yaɗa Labarai, Kwamitin Shirya Fareti, Kwamitin Shirya Lacca, Kwamitin Saukar Manyan Baƙi da Kwamitin Sakateriya.

Akwai mambobi irin su Femi Gbajabiamila, Shugabar Mai’aikatan Gwamnatin Tarayya, Folasade Yemi-Esan, Ministan FCT Nyesom Wike, Ministan Harkokin Kuɗaɗe, Wale Edun, Ministan Yaɗa Labarai Mohammed Idris, Ministan Tsaro Badaru Abubakar, Ministan Gona Abubakar Kyari, Ministan Albarkatun Ƙasa da Ma’adinai, Dele Alake, Ministan Makamashi Adebayo Adelabu, Ministan Ayyuka, Dave Umahi, Ministan Harkokin Cikin Gida, Olubunmi Tunji-Ojo.

Sauran sun haɗa da Ministan Lafiya Umar Fate, Ministan Harkokin Mata, Uju Kennedy-Ohanenye, Hadiza Bala-Usman da sauran su.

Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button