Kannywood
Gwamnatin tarayya ta naɗa Rahama Sadau muƙami
Gwamnatin shugaban kasar bola Ahmed tinubu ta nada jaruma rahama Sadau mukami a cikin gwamnatin sa mukamin “shirin samar da arziki ta hanyar bunkasa basira na IDICE”.
Md Ali Nuhu kuma fitaccen jarumi masana’atar Kannywood shine ya fitar da wannan sanarwa a shafinsa na sada zumunta Instagram inda yake taya jarumar murna samun wannan mukami.
Ɗinbin masoya, iyaye da yan uwana da abokan sana’arta sun taya ta murna samun wanann mukami wanda za’a iya cewa wannan shine karon farko da rahama sadau ta samu mukami a gwamnatin tarayya.
A halin yanzu da ake ciki su biyu ne da sunka samu manya mukami a cikin gwamnatin shugaban Bola Ahmed tinubu ita da Ali Nuhu.