Labarai

Farashin Kayan Abinci Ya Fara Sauka A Kasuwanin Jihar Katsina

Tun bayan saukar farashin dala a Najeriya ake cigaba da samun saukin wasu daga cikin kayayyakin masarufi a kasuwanin Arewacin Najeriya.

Ga yadda farashin yake a wasu kasuwanin jihar Katsina :

1- Buhun masara fara – 58,000
2- Buhun Dawa – 51,000
3- Buhun Gero – 57,000 Dauro – 57,000
3- Buhun Gyada tsaba – 100,005 mai bawo – 35,000
4- Buhun Shinkafa tsaba – 120,000 ta tuwo – 130,000
5- Buhun Wake – 100,005 ja – 120,000
6- Buhun waken suya – 61,500
7- Buhun Dabino – 180,000
8- Buhun Dankali – 25,000
9- Buhun Tattasai – 22,000
10- Kwandon Tumatur kauda – 70,00,000

11- Buhun Tarugu – solo – 35,000
12- Buhun Albasa – 20,000
13- Buhun Kubewa busassa – 50,000
14- Buhun Alkama – 65,000
15- Buhun Taki yuriya – 37,000
15- Buhun Sobo baki – 28,000
16- Buhun Dankalin Turawa – 80,000
17- Buhun Sobo baki – 28,000
18- Buhun Dankalin Turawa – 80,000

Rahoto : Aisha Abubakar Ɗanmusa.

Wani Labari : ‘Yan bindiga sun kai hari ƙauyen Zamfarawa, sun sace mutum 28 ciki har da Mata da ƙananan yara a jihar Katsina

A ƙalla mutane kusan 28 ne tsakanin maza da mata da ƙananan yara masu garkuwa da mutane suka yi awon gaba da su, a ƙauyen Zamfarawa na ƙaramar hukumar Batsari da ke jihar Katsina.

Kamar yadda Katsina Reporters ta samu, a daren ranar Alhamis 18 ga watan Afrilu, 2024, ‘yan bindigar suka kai harin a yankunan na Batsari.

Ɓarayin dai sun daɗe suna addaba mutanen yankin inda kusan kowace rana sai sun kawo hari sun ƙwashi dabbobi tare da yin garkuwa da mutane domin karɓar kuɗin fansa.

Ƙaramar hukumar Batsari a jihar Katsina na cikin gagaruruwan da suke fama da matsalar tsaro wanda ɓarayin daji suke hana al’umma sukuni.

Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button