Kannywood

Ali Jita ya magantu kan abin da Adam a zango yace akan su

Fitaccen mawaki a masana’atar Kannywood kuma shugabantan murya daya ta kannywood Ali isah Jita ya yi wannan sako na musamman zuwa ga dan uwan sana’arsa adam a zango.

Adam a zango yan kwanakin nan ya fito yana rubuce-rubuce da kuma bidiyo na nuna irin rashin ko oho akan yadda wasu jaruman masana’atar Kannywood sunkayi da shi bayan ya taimakesa inda ya fadi harda Ali jita.

Ali jita shine yayi wani dan gajeren bidiyo inda yake mai cewa

“Wannan sako ne musamman zuwa ga adamu zango wanda nine shugaban kungiyar murya daya ta mawakan kannywood a Nijeriya baki a matsayina na Ali jita da yawun yan kungiya irin su nazifi Asnanic, Abubakar sani da ado Gwanja ina amfani da wannan dama da na baiwa adamu hakuri akan abubuwan da yace, muna cikin mutanen da ya taimawaka hakika haka yake.

Adamu mutumin kirki ne, zuciyarsa tana da kyau kuma ya taimaki mutane ba ma mu kadai ba da yawa a baya.

Lokaci yayi da yakamata da yan fim da mawaka muga ya zamuyi muja adamu a jiki , mugane minene matsaloli, mugane kuskure a baya mu gyara domin gaban tayi kyau.

In sha Allah idan ya dawo zamu zauna a kungiyance mugani a gyara.

Na biyu in bashi shawara akan

“Mutane baka iya musu sai kayi hakuri da abinda zasu ce, kama kau da kai da abubuwan da ke faruwa lokaci yayi na ka sanya karfi wajen goben shi wanda abu ne da zamuyi , in munzo mu da shi muga tayaya zamuyi.

Yana da kyau ka hakura da abubuwan da mutane zasu gayama nasan angayamaka haka ba sau daya ba, kuma ka manta abun da ya faru a baya ka nufaci gabanka.

Ina mai baka hakuri Allah ya sanya zuciyarka , duk damuwa da ke ciki Allah ya yaye , kuma munyi kuskure dan adam ajizi ne kayi hakuri , Allah ya dawo da kai lafiya nagode – ali jita.

Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button