Labarai

Ɗangote Zai Gina Katafaren Kamfanin Siminti A Jihar Gombe

Shahararren dan kasuwa kuma mai arzikin Afrika na daya, Alhaji Aliko Dangote ya yi alkawarin gina kamfanin siminti a jihar Gombe.

Alhaji Aliko Dangote ya bayyana haka ne yayin bikin auren ‘yar Alhaji Umaru Kwairanga a jihar Gombe.

Mai taimakawa gwamnan jihar Gombe a harkar yada labarai, Isma’ila Uba Misilli ya fitar da sanarwa a shafinsa na Facebook cewa Dangote ya ce zai kafa kamfanin ne lura da yadda al’amuran kasuwanci ke bunkasa a jihar.

Ya kara kuma da cewa gwamnan jihar ya samar da yanayi mai kyau da zai taimakawa kasuwanci wurin habaka da kuma irin yadda jihar ke da sinadarin hada siminti sosai.

Dangote ya tabbatar da cewa idan suka fara hada siminti a jihar Gombe akwai yiwuwar farashin siminti zai sauka a yankunan da su ke kewaye da Gombe.

Za a samu wannan rangwame ne saboda rage nisan jigilar simintin da za a samu.

Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button