Labarai

Ƙananan Yan kasuwa kimanin 1,291 za’a baiwa tallafin ₦50,000 – Minista



Ƙananan ‘Yan Kasuwa Kimanin 100,000 Sun Karbi Tallafin N50,000
Daga Shugaban Kasa Tinubu -Inji Ministar Kasuwanci

Ministar Masana’antu, Ciniki da Zuba Jari, Doris Uzoka-Anite, ta bayyana cewa, ‘yan kasuwa Kimanin 100,000 a fadin tarayyar kasar nan ne suka Karbi Naira 50,000 ta hanyar tsarin bayar da tallafin sharadi na Shugaban kasa, Wanda kuma aka fi sani da Shirin Tallafin Kasuwanci.

Ƙananan Yan kasuwa kimanin 1,291 za'a baiwa tallafin  ₦50,000 -  Minista
Doris Uzoka-Anite

Ministar, wacce tayi magana ta bakin mai taimaka mata, Terfa Gyado, ta tabbatar da cewa an fara rabon kudaden ne makonnin da suka gabata, Kuma za a raba wa masu ƙananan sana’o’i kimanin 1,291 a kowace karamar hukuma.

Gwamnatin Tarayya ta sanar da Shirin Ba da Tallafin Sharadi na Shugaban Kasa a cikin Disamba 2023 don karfafawa kananan Yan Kasuwa Kudaden da aka Ware sun Kai Naira Biliyan 200, za a raba sune ta hannun bankin masana’antu don tallafa wa masana’antun da ‘yan kasuwa a fadin ƙasar nan.

Wannan ci gaban ya zo ne watanni takwas bayan da Shugaba Tinubu ya sanar da bayar da tallafin ga masana’antun da masu kananan sana’o’i, da kuma makonni biyu bayan an umurci masu bukatar su gabatar da NIN nasu a matsayin wani bangare na bukatun da ake bukata don samun tallafin da aka ware domin rage tasirin da sauye-sauyen tattalin arzikin da aka yi a baya-bayan nan.

Liberty Tv









Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button