YANZU YANZU: Ƴan bindiga sun sace ɗaliban firamare tare da harbin wasu a Kaduna
Ƴan bindiga sun afka cikin wata makarantar firamare ta Kuriga (1) da ke karamar hukumar Chikun ta jihar Kaduna, inda suka yi awon gaba da dalibai da dama.
Kawo yanzu ba a iya tantance adadin ɗaliban da aka sace ba, amma mazauna yankin sun ce kusan 100 ne.
Rahotanni sun ce shugaban makarantar da wasu malamai na cikin wadanda abin ya shafa.
Daily Trust ta tattaro cewa lamarin ya faru ne da karfe 8:20 na safe bayan kammala asambile a yau Alhamis, kamar yadda majiyarmu ta daily Nigerian Hausa na ruwaito.
Wani mazaunin garin, Shitu ya tabbatar da faruwar lamarin, inda ya ce galibin daliban sun tsere daga ajujuwan su a lokacin da suka hango ƴan bindigar a harabar makarantar.
Daily Trust ta ce ta kasa samun Jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan jihar, ASP Mansir Hassan a waya, kuma har ya zuwa lokacin haɗa rahoton bai amsa sakon kar-ta-kwana da aka aike masa ba.