Sheikh Ibrahim Khalil ya bukaci gwamnan Kano ya bada murja kunya muƙami
Sanannen malamin addinin musulunci, Sheihk Ibrahim Khaleel, ya bukaci gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, da ya nada , Murja Ibrahim Kunya yar Tik Tok,a matsayin babbar mataimakiya ta musamman kan kafafen sadarwa na zamani.
Sheikh Khalil ya yi wannan kiran ne a ranar Lahadin da ta gabata a cikin wani shiri da yagabatar a tashar Freedom Radio da ke Kano, kamar yadda majiyarmu ta dclhausa na ruwaito.
Malamin yace yin hakan zaitamakawa gwamnati da al’umma kwarai da gaske wajen,tallafawa mata musamman yan social media ta yadda za’a fito da sabbin hanyoyin kasuwanci na zamani da zai taimaka ta shafukan sada zumunta.
A kwanakin baya ne Hukumar hisbah ta jihar kano ta gurfanar da murja Ibrahima a gaban wata kotun shari’ar Musulunci karkashin jagorancin Nura Yusuf Ahmad ta bayar da umarnin cewa, Murja Ibrahim Kunya a kaita asibiti domin ayimata gwajin tabin hankali a wani asibitin gwamnati domin sanin halin da take ciki.