“Saura Kiris Ku Ji Daɗi” Shugaba Tinubu Ya Aike da Saƙo Ga Ƴan Najeriya, Ya Kaddamar da Sabon Shiri
Bola Ahmed Tinubu ya ƙara kwantar da hankulan ƴan Najeriya game da wahalhalun da suka shiga na yunwa Shugaban ƙasar ya tabbatar da cewa gwamnatinsa za ta fito da ƙarin kayan abinci kuma nan bada daɗewa ba abubuwa zasu fara kyau Ya ce gwamnatinsa ta shirya tallafawa mata domin suna daga cikin masu rauni da ke buƙatar a agaza masu
Shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu, ya tabbatar wa ƴan Najeriya cewa nan bada jimawa ba abubuwa za su fara sauyawa zuwa farin ciki a Najeriya. Shugaban ƙasar ya ba da wannan tabbaci ne yayin da ƴan Najeriya ke fama da wahalhalun tsadar rayuwa sakamakon wasu sauye-sauyen gwamnati, The Cable ta rahoto.
Bola Tinubu ya ce yana sane da cewa ‘yan Najeriya na korafi kan yunwa, inda ya kara da cewa gwamnatinsa ta fito da kayan jin kai domin a magance illolin yunwa.
Shugaban ya kuma ce gwamnatinsa a shirye take ta aiwatar da sabon mafi karancin albashi, kamar yadda The Nation ta rahoto. Tinubu ya kaddamar da sabon shiri na mata Tinubu ya bayyana hakan ne a ranar Alhamis, 7 ga watan Maris, a fadar shugaban ƙasa da ke Abuja, yayin bikin kaddamar da shirin mata na Najeriya. Ya ce: “Gwamnatina zata tafi da mata kuma wannan na ɗaya daga cikin tsare-tsare na, ina alfaharin tsayawa a gabanku yau kuma na gaya muku cewa goben matan Najeriya za ta yi kyau. “A matsayinmu na gwamnati aikinmu ne mu ba da fifiko ga ’yan ƙasa masu rauni waɗanda sune mata da kananan yara.”
Yaushe ƴan Najeriya zasu samu sauƙi?
Da yake tsokaci kan halin yunwa da ake ciki, Shugaba Tinubu ya ce gwamnatinsa zata yi duk mai yiwuwa ta hanyar samar da tallafi domin al’umma su ci su ƙoshi.
“A yau ana nuna damuwa kan yunwa, zamu fito da kayan abinci domin kawar da duk wata illa ta yunwa, abubuwa sun yi wahala amma ba zamu zauna dindindin a haka ba. “Nan bada daɗewa ba abubuwa za su fara canzawa saboda zamu fito da ƙarin abinci ga al’umma, sannan a shirye muke mu aiwatar da sabon mafi ƙarancin albashi.”
~Liberty