Labarai

RAƊAƊIN TSADAR RAYUWA: Dalilin da yasa Gwamna Abba kabir keson a buɗe boda

Advertisment

Gwamna Abba Yusuf na Jihar Kano ya roƙi Shugaba Bola Tinubu ya gaggauta buɗe kan iyakoki, domin a samu damar shigo da kayan abinci, ta yadda za su samar wa jama’a rangwamen matsananciyar wahalar tsadar rayuwar da su ke fama da ita.

Wannan roƙo ya na cikin wata sanarwar da Mai Magana da Yuwun Gwamnan Kano, Sanusi Bature ya fitar a ranar Litinin, bayan da Gwamna Yusuf ya karɓi baƙuncin Shugaban Hukumar Kwastan na Ƙasa, Adewale Adeniyi, a Gidan Gwamnatin Jihar Kano.

Gwamna Yusuf ya nuna damuwa da rashin jin daɗin yadda wasu tsare-tsaren gwamnatin tarayya kamar rufe kan iyakoki suke ci gaba da kassara jama’a, lamarin da ya ce hakan ya ƙara zuguguta hauhawar farashin kayan abinci da sauran fannonin tsadar rayuwa, musamman kayan masarufi a faɗin ƙasar nan.

“Mu na jinjina wa Shugaban Ƙasa dangane da shirin ɗaukin abinci da ake kan yi, wanda ya sa Kano ce za a ƙaddamar da shi. Abba ya ce ya yi amanna shirin zai sauƙaƙa wahalar abinci idan aka yi aiki da shi,” haka sanarwar ke ƙunshe.

“Sai dai kuma wani gagarumin abin da samar da wadatar abinci da sauƙin farashin sa a cikin gaggawa, shi ne idan Shugaban Ƙasa ya bada umarnin buɗe kan iyakoki cikin gaggawa, domin a samar da damar da kayan abinci za su shigo da sauran kayan masarufi.

“Gwamna Yusuf ya nuna cewa irin wahalar da ake sha musamman a cikin azumi ta zama babban dalilin da ya wajaba a buɗe kan iyakoki, domin jama’a su samu sauƙin ƙuncin rayuwa.”

Daga nan kuma Gwamna ya gode dangane da umarnin da yadda Hukumar Kwastan ta shirya raba kayan abincin da aka ƙwace ga al’ummar Jihar Kano.

Daga nan ya roƙi Shugaban Kwastan ya yi bakin ƙoƙarin ganin cewa kayan abincin da za su raba ɗin sun isa ga waɗanda za a raba don su.

Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Advertisment
Back to top button