Labarai

Nijeriya ta zama dandalin mutuwa al’umma a ƙarƙashin mulkin Apc da Tinubu – Atiku Abubakar

Advertisment

Tsohon mataimakin shugaban ƙasa Atiku Abubakar ya yi Allah-wadai da harin ta’addancin da aka kai a ƙaramar hukumar Rafi ta jihar Neja. An dai kai harin ne a ƙauyen Madaka wanda ya yi sanadiyyar rasuwar Magajin Garin da wasu mutum 20.

Da yake mayar da martani game da harin, Atiku a cikin wani rubutu da ya yi a shafinsa na X (wanda a baya aka fi sani da Twitter) a ranar Juma’a, ya ce Najeriya ta zama “filin mutuwa” a ƙarƙashin Shugaba Bola Tinubu.

Muryaryanci ta ruwaito cewa,Ya yi kira da a gaggauta samar da ƴan sandan jihohi. A kalamansa: “Abin takaici ne yadda Najeriya ta zama filin kisa. Kashe mutane da dama da suka haɗa da Magajin Gari, a ranar Alhamis da kuma sace wasu da ba a tantance adadinsu ba da wasu ƴan bindiga suka yi a ƙauyen Madaka da ke ƙaramar hukumar Rafi a jihar Neja, wani tabbaci ne cewa saɓanin tabbacin da ake bayarwa, matsalar rashin tsaro na ci gaba da taɓarɓarewa a ƙasar mu.

“Dole ne mu ba da fifiko kan tsaro tare da hanzarta aiwatar da gyaran kundin tsarin mulki wanda zai samar ƴan sandan jihohi ta yadda jihohi da ƙananan hukumomi za su iya fito da hanyoyin da suka dace da yankinsu wajen magance wannan matsalar rashin tsaro a ƙasar mu. “Ina alhini da addu’a ga iyalan waɗanda suka rasu da kuma gwamnati da al’ummar jihar Neja.”

Advertisment






Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button