Labarai

Na sauka daga muƙamin hisbah – Sheikh Aminu Daurawa

Bayan irin abubuwan da suke faruwa akan irin ayyukan da hukumar hisbah take karkarshin kwamanda Sheikh Aminu Ibrahim daurawa na operation dauka badala inda ake ta kamo mata da maza da sauransu wanda abubuwan ba’a cewa komai.

Babban kamun da yafi daga hankali al’umma shine kama wata fitacciyar yar tiktok murja kunya wanda nan take hisbah na kai ta kotu daga nan anka sake ta, bayan korafi da yayi yawa sai anka sake kama ta.

Daga nan gwamnan jihar kano engr Abba Kabir Yusuf yayi magana acewa akwai Kurakurai akan ayyukan da hukumar ita hisbah keyi, wanda a yau din nan mun samu sakon sauka daga mukami daga bakin shehin malami Sheikh Aminu Ibrahim daurawa wanda shine kwamandan hisbah.

“Assalamu alaikum warahamatullah yau muna ashirin ga watan sha’aban 1445, wanda yazo daya ga watan march, 2024 ina daga nan jihar Kaduna inda muke gabatar da taro da yan majalisa karkashin sipika yadda za’a gabatar da doka wacce zata wajabta kwajin lafiya kafin aure a jihar kano kamar yadda sauraran jahohin Nijeriya sunka sun kayi irin wannan doka.

To dazu sai naji wasu jawabai suna ta fitowa daga jihar kano wadanda a gaskiya sun kashe min gwiwa, abinda nake ta kokari naga na gabatar a hisbah shine gyaran tarbiyya da gyaran hali, kuma nayi iya yina wajen gayyatar masu finafinai nayi zama da su, na basu shawarwari, munyi maganganu da yawa akan yadda za’a gyara tarbiyya al’umma ta yarda ake gabatar da fina finai Waɗanda sunka saɓawa al’ada da addini da zamantakewar mu.

Haka na kira yan tiktok na dauki kudina cikin aljihuna da mataimakana munka haɗa munka basu kudin data da kudin mota munka zauna da su munkayi shawarwari, haka kuma na gayyato murja da yan uwanta masu yin tiktok mun zauna da su na basu shawarwari na yi musu nasiha ta hanyar da zasu bi su natsu su koma hayacin su.

Daga baya wadanda basu ji ba sunka koma suka cigaba da abubuwan da suke yi wanda yake taɓa tarbiya yake ɓata halaye kuma munyi iya ƙokarin mu ,muga cewa munyi abinda ya kamata , to amma ina bada mai girma gwamna hakuri bisa fushi da yayi da maganganu da ya fada kuma ina rokon yayimin afuwa na sauka daga kan wannan mukami da ya bani na hisbah.

Kuma ina masa addu’a ina masa fatan alkhairi Allah ya bashi nasara Allah ya taimake shi ya taimaki gwamnatin sa, Allah ya daukaka addinin musulunci.

Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button