Na gamsu da alkiblar gwamnatin Tinubu da Shettima – Buhari
Duk da irin matsalar tattalin arziki da Nijeriya ke ciki da ma matsalar tsadar rayuwa da ake fama da ita a kasar tsohon shugaban Nijeriya Muhammadu Buhari ya ce ya gamsu da alkiblar da shugabannin siyasa na yanzu suka fuskanta.
Buhari ya bayyana haka ne a lokacin da ya karbi bakuncin mataimakin shugaban kasa Kashim Shettima a garin Daura na jihar Katsina a ranar Asabar, jaridar Dclhausa na ruwaito.
Tsohon shugaban kasar ya yabawa gwamnatin Bola Tinubu bisa kokarin da take yi na daidaita tattalin arzikin kasar.
Wani Labari : Na Yi Murna Da Tinubu Ya Ƙara Farashin Man Fetur – Buhari
Tsohon shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya bayyana cewa ya yi murna matuƙa da shugaban ƙasar na yanzu, Bola Ahmed Tinubu ya ƙara farashin man fetur a ƙasar.
Buhari ya faɗi haka ne a yayin wani taro da ƙungiyar tuntuɓa ta jihar Katsina ta shirya da manufar ƙaddamar da yaƙi da tu’ammali da miyagun ƙwayoyi a tsakanin ƴan jihar.
Jaridar Jakadiya na ruwaito,a yayin taron wanda ya gudana a ranar Lahadin nan a fadar gidan gwamamtin jihar ta Katsina, cikin raha da barkwanci tsohon shugaban ya ce,…