Labarai

Matsin Rayuwa : Garin kwaki na neman gagarar talakawa da ake yi domin su

Farashin garin kwaki ya ƙaru da kashi 50 bisa 100 a garin Enugu, jihar da ake sarrafa shi haiƙan, kuma ana ganin a irin can ne ma ya kamata a ce an samu sauƙin farashi.

Yayin da garin kwakin wanda ake wa kallon cimar talakawa ne ya ƙara tsadar da ya ke neman ya gagari, talakawan, ita ma shinkafa ta ƙara tsadar da idan ka saya kwana biyu baya, muddin ka koma kasuwa a yau, to idan ka ji farashin, sai dai ka koma gina ka sake dabara, ko ‘yan dabaru.

Binciken da aka yi a garin Enugu ya nuna cewa yawancin waɗanda ke sayen mudu-mudu a baya, yanzu lamarin ya gagare su, sun koma sayen kofi-kofi.

Lita 5 na garin kwaki, wato cikin bokitin fenti ɗaya, wanda a cikin Janairu ake sayarwa Naira 2,000 zuwa Naira 2,200, to daga ranar Lahadi da ta gabata ya koma Naira 2,700.

Su ma marasa galihun da ba su iya sayen mudun garin kwaki, ɗan kofi ɗaya ko kofi biyun da suke saye a yanzu ya tashi zuwa Naira 150 duk kofi ɗaya, har Naira 200.

Yayin da wakilin mu a Kano ya ji wani ya na cewa, “Ni dai gara na sayi kofin garin rogo Naira 200 da a ce na bayar da Naira 400 a ba ni Indomi guda ɗaya. Idan teburin mai shayi na je, sai na bada Naira 500 za a dafa min Indomi ɗaya. Wannan rayuwa ya ake so mu yi ne?”

Buhun garin kwakin da ake sayarwa Naira 18,500 cikin watan Janairu a Enugu, daga ranar Lahadi ya koma Naira 29,000.

Buhun shinkafar waje wadda a cikin watan Janairu ake sayarwa Naira 55,000 zuwa Naira 60,000, yanzu ya koma Naira 80,000.

Wata mata mai suna Bridget Ugwu da ke sayar da garri a Sabuwar Kasuwar Enugu, ta ce hanya ɗaya da za a sauko da farashin gari ita ce a faɗaɗa noman rogo ta hanyar ƙara share dazuzzuka, domin a samu wadatar gonaki. Sannan kuma a daina fitar da shi kasashen da ke maƙautaka da mu.

Ita kuwa Ochuba Ozor da ke sayar da shinkafa, ta ce a yanzu sai ta ɗauki lokaci mai tsawo ba a sayi shinkafa ba a rana. Ta ce amma kafin ta yi tsada, har tururuwa ake yi ana layin saye a wurin ta.

Tuni dai talakawa suka fara tare manyan motocin dakon kayan abinci su na daka wasoso a garuruwa daban-daban a faɗin ƙasar nan.

Ko a ranar Lahadi, PREMIUM TIMES Hausa ta bada labarin yadda dandazon hasalallu, mayunwata da mabuƙata suka fasa gidan ajiyar kayan tallafi, sun daka wasoson kayan abinci a Abuja.

Wasu mazauna garin Karimo da ke gundumar Babban Birnin Tarayya, FCT Abuja, sun fasa katafaren rumbun ajiyar kayan tallafin abinci, suka daka wasoson abin da kowa zai iya ɗiba.

Lamarin ya faru a ranar Lahadi, wajen 7 na safe, har zuwa 9 na safe mutane na jidar kayan abinci.

An fasa rumbun ajiyar kayan abincin ne a daidai lokacin da raɗaɗin tsadar rayuwa da tsadar kayan abinci ke nuƙurƙusar ‘yan Najeriya.

A wasu garuruwa kuma, ana tare motocin da ke ɗauke da lodin kayan abinci ne ana wasoso ƙarƙaf.

Matsalar tsadar rayuwa dai ta samo asali tun bayan cire tallafin fetur da Shugaba Bola Tinubu ya yi, tun a ranar 29 ga Mayu, 2023, ranar da aka rantsar da shi.

Ko cikin wannan makon ma sai da Tinubu ya ce ‘cire tallafin fetur ya zama ciwon ido, sai dai a yi haƙuri kawai.’

Rahotanni sun tabbatar da cewa ko a lokacin kullen korona sai da mabuƙata suka fasa rumbun ajiyar kayan abincin a cikin 2020.

Hakan na nuna cewa ba wannan ne karo na farko da hasalallu su ka fara fasa rumbun ajiyar kayan tallafin ba.

Jami’an ‘yan sanda sun shaida wa Daily Trust cewa jami’an su sun isa wurin, kuma komai ya koma kamar kullum.

Cikin makon jiya ne Ƙungiyar Ƙwadago ta Ƙasa ta yi zanga-zangar lumana a faɗin ƙasar nan, domin nuna damuwa dangane da mawuyacin halin tsadar rayuwa da tsadar kayan abinci da ake fama da su a ƙasar nan.

~Premium Times Hausa

Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button