Madallah: An saki Daliban Makarantar kuriga da ‘yan bindiga suka sace a Kaduna
Gwamnan Jihar Kaduna ya bayyana hakan a cikin wata sanarwa ta musamman Yana Mai cewa Da sunan Allah mai rahama mai jinkai ina sanar da cewa an sako yaranmu na makarantar Kuriga.
Godiya ta musamman ga mai girma shugaban mu, Bola Ahmed Tinubu, GCFR, bisa ba da fifiko ga tsaro da tsaron ‘yan Nijeriya, musamman tabbatar da ganin an sako yaran makarantar Kuriga da aka sace ba tare da wani lahani ba. Yayin da yaran makarantar suke zaman jira, na yi magana da Mr. Shugaban kasa sau da yawa. Ya yi bakin ciki ya yi mana Jaje kuma yana aiki dare da rana tare da mu don tabbatar da dawowar yaran lafiya,kamar yadda majiyarmu ta jaridar mikiya na ruwaito.
Dole ne kuma a yi godiya ta musamman ga dan uwanmu mai ba da shawara kan harkokin tsaro, Mal. Nuhu Ribadu bisa jagoranci nagari da kwana babu barci da Mal. Dabarun Ribadu tare da daidaita ayyukan hukumomin tsaro, wanda a karshe ya haifar da wannan nasara Abin Ayaba ne.
Sojojin Najeriya kuma sun cancanci yabo na musamman don nuna cewa tare da jajircewa, Kwazo domin ganin an lalata masu aikata laifuka tare da dawo da tsaro a cikin al’ummominmu.
Muna kuma godiya ga daukacin ‘yan Najeriya da suka yi addu’a kan Allah ya dawo da ‘yan makaranta lafiya. Lallai wannan ranar farin ciki ce. Muna godiya fa Allah Ta’ala Mai dukkan daukaka.