Hukumar Anti-Corruption ta Kano ba ta da ikon bincikar Ganduje – Babbar Kotun Tarayya
Babbar Kotun Tarayya d ake jihar Kano ta yanke hukuncin cewa hukumar yaki da cin hanci da rashawa ta Kano da ake wa lakabi da Anti-Corruption ba ta da ikon a bisa doka na binciken tsohon gwamnan jihar kan bidiyon Dala.
Alkali Abdullahi Muhammad Liman shi ne ya sanar da wannan hukunci a Talatar nan wanda ya ce laifin da ake zargin tsohon gwamnan da shi ya fada cikin laifuka da hukumomin gwamnatin Tarayya ke da hurumin bincikarsu.
Wani labari : ‘Yan sanda sun haramta amfani da na’urar cire kudi ta POS ko ‘transfer’ a caji ofis
Rundunar ‘yan sandan Nijeriya ta sake nanata batun nan na haramta amfani da na’urar cire kudi ta POS da duk wani nau’in tura kudi a zamanance ‘bank transfer’ a cikin caji ofis da sauran ofisoshin ‘yan sanda a duk fadin kasar.
Hakan ya biyo bayan zarge-zargen da ke tasowa cewa ana hada-hadar kudi ta hanyar amfani da na’urar POS ko ‘transfer’ da sa hannun wasu bare-gurbin ‘yan sanda.
Wannan haramci dai na da nufin kare kima da martabar aikin ‘yan sanda da hana yunkurin karbar cim hanci a duk ofisoshin ‘yan sanda na kasar.
A cikin wata sanarwa daga mai magana da yawun rundunar ‘yan sandan Nijeriya ACP Olumuyiwa Adejobi, ta ce babban sufeton ‘yan sanda na kasa IGP Kayode Egbetokun ya ja kunnen masu aikata hakan cewa za su kuka da kansu idan aka kama su.