Labarai

Gwamnatin Tarayya ta baiyana Mamu da wasu mutane 15 a matsayin masu ɗaukar nauyin ta’addanci

Advertisment

Rahotanni sun bayyana cewa gwamnatin tarayya ta bayyana sunan Tukur Mamu, mawallafin jaridar Desert Herald a matsayin daya daga cikin wadanda ake zargi da hannu wajen ɗaukar nauyin ta’addanci a ƙasar.

Mamu, a cewar wani rahoto da jaridar The Punch ta fitar, an jera shi ne cikin kungiyoyi 15, da suka hada da mutane tara da kuma Kamfanonin Canjin Kuɗi, BDC, guda shida.

A cikin rahoton, jaridar Punch ta buga wata takarda daga Sashin kula da Harkokin kudi na sirri na Najeriya, NFIU.

A cewar takardar, kwamitin takunkumi na Najeriya ya gana ne a ranar 18 ga watan Maris inda aka ba da shawarar sanya sunayen wadanda aka ambata a baya, biyo bayan ɗaukar nauyin ta’addanci.

NFIU ta ce Mista Mamu, “ya shiga harkar tallafawa ayyukan ta’addanci ta hanyar karba da bayar da kudaden fansa, kan kudi dala dubu 200, domin tallafa wa ‘yan ta’addar ISWAP don sako mutanen da suka yi garkuwa da su a harin jirgin kasa na Abuja zuwa Kaduna”.

A halin yanzu dai Mamu yana fuskantar shari’a a gaban gwamnatin tarayya bisa zargin taimakawa ‘yan ta’addan da suka kai hari kan jirgin Abuja zuwa Kaduna a watan Maris din 2022.

Sannan rahoton, ya nuna sauran ɗaiɗaikun mutane da kungiyoyi da su ke daukar nauyin ta’addanci.

~ Daily Nigerian Hausa

Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Advertisment
Back to top button