Labarai

Gwamna Abba yana son Hisbah, wasu shaiɗanu ne su ka haɗa wannan fitinar — Sheikh Daurawa

Kwamandan Hisbah na Jihar Kano, Sheikh Aminu Daurawa, ya bayyana cewa sun fahimci ashe Gwamna Abba Kabir Yusuf na jihar yana son Hisbah da ayyukan ta.

A cewar Sheikh Daurawa, wasu shaiɗanu ne su ka haddasa wannan fitinar da ta kunno kai, inda ya kara da cewa ” amma a jiya duk an doke waɗannan shaiɗanu.”

Da ya ke ganawa da manema labarai a harabar hukumar ta Hisbah bayan ya koma ofishin sa a matsayin Kwamanda a yau Talata, Daurawa ya zargi wasu “shaiɗanu” da turawa gwamnan Kano bidiyon da ake zargin jami’an hukumar suna aiki ba daidai ba.

A cewar Sheikh Daurawa, Gwamna Abba ya karbi malamai da dattijan da su ka jagoranci zaman sulhun da aka yi bayan da ya baiyana murabus din sa a makon da ya gabata.

Ya kara da cewa Gwamna ya nuna aniyarsa ta zama ɗan Hisbah da kuma baiwa hukumar duk wani taimako da take bukata da suka haɗa da motocin aiki, karin albashi da canja kakin aiki.

“Wasu shaiɗanu ne suka turawa gwamna bidiyon da ta wuce ma yan watanni a baya domin kawai su sanya wa gwamna tsabar Hisbah.

“Sun yi hakan ne a lalata aikin Hisbah su kuma su samu damar dawo da baɗala a Kano. So ake a mayar da Kano ta zama garin ƴan daudu, ƴan maɗigo, zina da luwadi.

“To a jiya dai waɗannan shaiɗanu sun ji kunya domin an daidaita dukkanin al’amura,” in ji Daurawa.

Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button