Labarai

Gwaman Rivers Siminalayi ya biyawa maniyyata dukan cikon kuɗin hajjin bana 1.9 miliyan

Advertisment

Gwamnan jihar Rivers a kudancin Najeriya, Siminalayi Fubara, ya biya wa maniyyata aikin Hajjin bana daga jihar cikon naira miliyan daya da dubu dari tara na kuɗin kujerun.

A farkon makon nan ne Hukumar Alhazan Najeriya ta bayyana ƙarin kudin, tana mai alaƙanta matakin da faɗuwar darajar naira.

BBC ta ruwaito cewa Gwamnan dai ya dauki wannan mataki ne a kokarin cika alkawarin da ya yi wa jama’ar jihar a lokacin yaƙin neman zabe, cewa zai tafi da kowa a gwamnatin ba tare da nuna bambancin addini ko ƙabilanci ba.

Alhaji Yakubu Aliyu, daya ne daga cikin shugabannin ‘yan arewacin Najeriya mazauna jihar ta Rivers, kuma ya yi karin bayani, inda ya ce gwamnan ya biya wa daukacin maniyyata 41 da suka fito daga jihar Naira miliyan 1.9 ga konwannen su.

Aliyu ya kara da cewa Gwamna Fubara ya kuma sayi wasu kujerun aikin Hajjin guda 8 a kan sama da Naira miliyan 6 ko wacce ya rabawa musulman jihar.

“Dama gwamnan ya yi alƙawarin tun a lokacin yakin zaɓen sa cewa zai tafi da kowa a jihar ba tare da bambancin addini ko kabila ba

“Tun da fari ma, kujera 34 NAHCON ta baiwa Rivers, amma ya buga nan ya buga can sai da ya nemo karin kujeru 13, kaga kujeru 47 kenan.

“Hikimar hakan, shine domin baɗi a baiwa Rivers kaso mai yawa na kujerun aikin Hajji. Ya kuma yi kokarin ajiye daukacin kaso kujeru da aka baiwa jihar ta Rivers .

Advertisment






Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button