Labarai

Dr. Sani umar R/lemo ya magantu akan murabus din sheikh daurawa

A safiyar yau ne ash-sheeikh Aminu Ibrahim daurawa wanda shine kwamandan hisbah na jihar kano amma mai murabus ya fadi irin cewa yayi iya kokarinsa wajen nasiha, wa’azi da karantarwa akan gyaran tarbiyya da gyran hali wanda tabbas sunyi iya kokarin su duniya ta shaida.

Sai kwatsam an ka samu wasu maganganu da mai girma gwamna abba Kabir Yusuf yayi cikin fushi akan irin abubuwan da ya nuna ɓacin ransa da hukumar hisbah take aikatawa da sunan operation dauka badala, akwai Kurakurai wanda shi ya sanya Sheikh irin kalamansa sun durkushe gwiwarsa ta sanadiyar hakan Sheikh Daurawa yayi murabus.

Ash Sheikh Dr. Muhammad sani umar R/lemo ya magantu akan wannan hukunci da ya dauka inda yake mai cewa.

“Malam Aminu Daurawa, Allah ya kara maka taufiki, ya karfafi gwiwarka, a kan duk ayyukanka na alheri, ya tsare ka daga duk wani abin ki.
Aikinka na yin umarni da kyakkyawa da hana mummuna, zai ci gaba da dorewa a matsayinka na malami mai karantarwa, ba zai tsaya ba har zuwa mutuwa in sha Allah. Allah ya cika mana burinmu na alheri. Amin.”

Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button