Beli : Mun haramta murja kunya wallafa komai a shafinta na Manhajar soshiyal midiya har sai an kammala shari’a – kotu


Babbar Kotun jihar Kano da ke zamanta a Bompai, ta bada belin fitacciyar mai amfani da shafin nan na Tik-Tok Murja Ibrahim Kunya, tare da gindaya mata wasu sharuɗa.
Kotun ƙarƙashin mai Shari’a Nasiru Saminu ce ta bada Belin Murja a yau Litinin, bayan da ta bincika wasu dokoki da suka kafa hukumar Hisba ta jihar Kano, wanda zai iya bada Belin nata.
Haka kuma matakin belin ya biyo bayan hutun da kotun zata tafi, inda ta sanya sharaɗi ga Murja Ibrahim Kunya, kan ta daina wallafa komai a shafukan ta na sada zumunta har sai an kammala Shari’a.
Har ila yau, kotun ta buƙaci Murja Kunya, ta kawo mutane biyu da za su tsaya mata, har ma ta umarci kwamishinan ƴan sandan Kano, da ya sanya ido kan Murja Kunya domin ganin bata karya doka ba.
Idan dai ba’a manta ba yanzu haka Murja Ibrahim Kunya, ta shafe tsawon kwanaki 35, cikin tuhumar da ake yi mata, wadda ta kai ga bincikar lafiyar Ƙwaƙwalwar ta a Asibitin masu taɓin Ƙwakwalwa