Abinda ya kamata ku sani akan ‘case’ din Amal Umar da saurayinta


Jaruma amal umar wadda yan sanda sunka gurfanar da ita akan zargin cin wasu makudan kudi daga saurayinta wadda kowa yake mamaki ya ta damfarare shi naira miliyan goma sha 13, mansurah isah itace ta zayyano abubuwan da ake wannan rikici a shafinta na sada zumunta ta lissafi abubuwa kusan hudu dauke da wasu karin bayyanai.
Ga abubuwan kamar haka .
1. 4 billion ake nema awajen mutumin
2. Dan crypto ne, kudin crypto yaci
3. Ba a lokaci daya ya saka mata 13 million ba, sunfi shekara daya suna tare, sannan a shekara dayan nan, transaction daya wakana a tsakanin su shine 13million.
4. Akwai wanda wannan mutumin ya turawa 100million, 200 da sauran su, baa kama su ba, baa kwace musu mota ko wani abu ba, wai sai wacce yake bawa 500 thousand naira, 1 million da saura su.
Dan haka kuyiwa kanku adalci, ya kamata a kama Amal ko a kwace mata mota a wannan case din ???
Sannan har an saka musu ranar aure fa, yana zuwa shop dinta siyan kaya, duk kudin nan ne in aka hada ya kai 13million.
Har wata motar ta ya taba siya a wajen ta.
Mu a matsayin mu na musulmai, mu dinga adalci a duk abinda zamu cewa wani, bai kamata kuyi zagi, sharri akan abinda baku sani ba.
In yar film ce sai mai ?? Saurayi baya kashewa budurwasa kudine? In saurayin ki yazo shop dinki siyan kaya, zaki ce bazaki siyar mishi ba dan kina tsoro zaace ya baki kudi ??
Akwai manyan manyan transactions da wannan mutumin yayi, wanda sufi 100 million a cikin wassu account,. Baa kama su ba.
Sannan sunyi amfani da Amal ne as a scapegoat wallah, sunga she’s innocent, and easy to blackmail.
Dan haka masu jin dadin hakan ya faru da ita, kuje gaku ga duniya nan, wanda suke mata kyakywan Fata kuma, Allah ya tsareku da sharrin mutane, hukuma da duniya ameen.