Labarai

Abin a yaba : Anyi nasarar Cafke barawon pos a jihar Kaduna

Cikin ikon Allah tareda taimakon Alumma a wannan kafar ta Facebook, tareda gidajen jaridun mu masu albarka munsamu nasarar Kama wannan azzalumin barawon POS a jihar Kaduna yanzu haka Yana a hannun Yan sanda a Rigasa Police Division.

Bayan nayi posting jiya gameda damfarar da wannan azzalumin yayimuna jiya, abun ya yadu sosai alumma sun taimaka muna matuqa wurin posting da sharing.

Dazu da safe misalin karfe 12 na Rana Ina zaune a office sai ga Kiran wani bawan Allah yacemun yaga posting din a jaridar Rariya yadauki number ta Kuma wlh ga mutumin Nan yagani a wani gidan abinci yayi zaune.

Nace mishi Dan Allah yaduba da kyau dai gudun kada asamu matsala yacemun wallahi shine, nace to Dan Allah yataimaka muna yaje police Station kusa dashi yayimuna reporting, haka akayi Yana zuwa ya hadani da DPO din wurin mukayi waya na fadamasa abunda yafaru duk tunanin su a jihar Kaduna muke nace mishi wlh a Zamfara ne.

Nan take suka fita da mota suka kamo shi, anyi masa tambayoyi bai musa ko daya ba, kuma ya shaida masu cewa akwai wani maigidan sa dake Zariya shi yake turawa kudin idan yayi satar POS din, Nan take DPO yasake kirana yace zasu sanya shi mota zuwa Zariya daga Kaduna domin akamo shi. Saboda binciken yagano zalunci alumma babu adadi ..

Ubangiji Allah ya cigaba da tona ma ire iren wadan nan miyagun mutane asiri.

Idan kasan ya zalunce ka ka tuntubeni kai tsaye domin hadaka da Yan sandan da yake hannun su….
07040818166

Isah Abdullahi Dankane
✍️

Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button
DOMIN SAMUN GARABASA