Labarai

Ɗalibai 9 cikin 21 sun kuɓuta a dan sace a jami’ar tarayya da ke Gusau

Advertisment

A ranar Juma’a ce ‘yan bindiga suka saki ɗalibai su 9 daga cikin su 21 da suka sace, waɗanda ke karatu a Jami’ar Tarayya da ke Gusau, Jihar Zamfara.

Ɗaya daga cikin masu shiga tsakani, wanda ya nemi a sakaya sunan sa, ya shaida wa PREMIUM TIMES cewa an saki ɗaliban su 9 bayan an shafe watanni huɗu cur ana gwagwata tattaunawa, ban-baki, lallashi da bada haƙuri.

Ɗaliban dai sun shafe kwanaki 178 a hannun ‘yan bindiga, tun bayan sace su da aka yi daga gidan kwanan ɗaliban jami’ar da ke Sabon Gida, kusa da Gusau a cikin watan Satumba.

A cikin daren ne maharan suka saci ɗaliban maza da mata da wasu mazauna unguwar. Sai dai kuma bayan sa’o’i da yin garkuwar, jami’an tsaro sun ceto wasu da aka gudu da su.

Mai shiga tsakani ya shaida wa PREMIUM TIMES cewa maharan sun sha nanata cewa sun yi garkuwa da su ne ba don a biya su kuɗin fansa ba, sai domin haushin gwamnatin tarayya da gwamnatin Zamfara sun kama ɗan’uwan gogarman ‘yan bindigar, Ali Kawaje.

Sai dai mai shiga tsakani ya ce lamari ya koma ɗanye tun bayan da Sojojin Saman Najeriya suka kashe Ali Kawaje a wani farmaki.

Majiyar ta ce sabon gogarman da ya gaji Kawaje ya ce ba zai saki waɗanda suka yi garkuwar da su ba.

“Sai da aka shafe makonni kafin mu gamsar da su tare da taimakon wasu shugabannin Fulani. Lokacin da muka koma tattaunawa tsakani, sun jajirce cewa su fa ba don kuɗi suke riƙe da waɗanda suka kama ɗin ba, amma saboda kawai an kama dangin su an tsare.

“Sun amince sun saki ɗaliban su 9, a bisa shiga tsakanin da wasu jagororin Fulani suka yi a tattaunawar”, cewar majiyar mu, wanda ba ya so a ambaci sunan sa.

Da aka tambayi majiyar ko an biya kuɗi kafin a saki ɗaliban, sai ya ce, “ai tun farko an ce ba don kuɗi aka kama su ba.”

“Mu aikin mu shiga tsakani, amma ba mu ma san sunan waɗanda suke so a sakar masu ɗin ba. Saboda haka ba mu yi wa gwamnati bayanin a biya kuɗi ba. Kuma ba a yi musayar fursunoni ba. Abin da zan iya shaida maka kenan,” inji shi.

An tsare ɗaliban a Dajin Babbar Doka, kusa da Jihar Kaduna. Amma an sake su a ranar Juma’a, aka damƙa su ga masu shiga tsakanin.

Mai shiga tsakani ya ce muna sa ran ba da daɗewa ba za su ƙara sakin wasu ma. Kuma da taimakon sa hannun da Mashawarcin Harkokin Tsaro na Musamman na Shugaban Ƙasa ke yi, za a saki sauran.

PREMIUM TIMES ta ji cewa an damƙa ɗaliban ga jami’an tsaro, su kuma za su damƙa su hannun gwamnatin jihar Zamfara a yau.

An tuntuɓi Kakakin Yaɗa Labaran Jami’ar Tarayya ta Gusau, Usman Umar, ya ce ba a sanar da shi wannan lamarin ba. Amma dai ya ji labarin sakin ɗaliban kamar yadda shi ma wakilin mu ya ji labari.

 

– Premium Times

Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Advertisment
Back to top button