Ƙasar Nijar ta yanke hulɗar soji da Amurka
Gwamnatin sojin Jamhuriyar Nijar ta sanar da yanke duk wata hulɗa da ta danganci haɗin-kai ta fannin soji da ƙasar Amurka “nan-take”.
Ta bayyana haka ne a wata sanarwa da kakakin gwamnatin Kanar Amadou Abdramane ya karanta ranar Asabar da maraice a gidan talbijin na ƙasar wato RTN.
Sanarwar ta ce daga yanzu Jamhuriyar Nijar ta katse duk wata dangantaka da Amurka wadda za ta sa sojojin ƙasar da ma fararen-hula da ke aiki da Ma’aikatar Tsaron Amurka su zauna a Nijar.
Lamarin na faruwa ne kwanaki kaɗan bayan wata tawagar jami’an gwamnatin Amurka, wadda ke ƙarƙashin jagorancin Mataimakiyar Sakataren Harkokin Wajen sashen Afirka, Molly Phee, ta je Nijar don ganawa da shugaban mulkin soji amma hakan ya gagara.
TRT AFRIKA HAUSA ta ruwaito cewa,Kanar Abdramane ya zargi jami’an gwamnatin Amurka da rashin bin ƙa’idojin diflomasiyya da kuma ƙin gaya wa gwamnatin sojin ƙasar mutanen da ke cikin tawagar da ta je Nijar.
A shekarar 2012 ne Amurka ta ƙulla yarjejeniyar haɗin-kai ta soji da Jamhuriyar Nijar inda kuma ta jibge dakaru kusan 1,000 a wani sansani da ke Agadez wanda aka ƙiyasta ya lashe kusan $100m.
Sakataren Harkokin Wajen Amurka, Antony Blinken ya kai wata ziyarar ba-zata Nijar, watanni huɗu kafin soji su kifar da gwamnatin Mohamed Bazoum.
Sojojin Nijar sun kori Faransa daga ƙasar bayan sun samu rashin jituwa da ƙasar da ta yi musu mulkin mallaka, sakamakon juyin mulkin da suka yi wa Bazoum a watan Yulin da ya gabata.
Kazalika sun soke yarjeniyoyi biyu kan harkokin tsaro da ƙasar ta ƙulla da Tarayyar Turai.
A watan Disamban da ya gabata sojojin na Nijar suka ƙulla yarjejeniya da Rasha wadda tuni ta kyautata dangantaka da Mali da Burkina Faso masu maƙwabtaka da ita.
~TRT AFRIKA HAUSA