Labarai

Ƙaramin yaro mai shekaru 13 a Jibia ya haddace Al-Qur’ani Maigirma



Wani Yaro mai shekaru 13 a Duniya dake zaune a ƙaramar hukumar Jibia, ya haddace Al-Qur’ani Maigirma a cikin Ɗalibai 53 da makarantar Tarbiyya ta yaye.

Kamar yadda Katsina Post ta samu, ɗalibin ya samu karatunsa a Makarantar Tarbiyyatul Islamiyya dake garin Jibia ta jihar Katsina, daga cikin ɗaliban akwai 31 daga ɓangaren Matasa da suka hada da Khuzaifa Mustafa Mansur mai shekaru 13 da haihuwa da kuma 22 daga ɓangaren Matan Aure.

Ƙaramin yaro mai shekaru 13 a Jibia ya haddace Al-Qur’ani Maigirma
Mahaddacen Al-Qur’ani

Walimar dai ta gudana a ranar Asabar 24 ga watan Fabrairu, 2024, a farfajiyar makarantar da ke Jibia a jihar Katsina.

Jaridar FBC ta ruwaito cewa, Ɗalibi Khuzaifa Mustafa Mansur mai shekaru 13 da haihuwa ɗa ne ga Malam Mustafa Mansur, fitaccen malamin addini ne a ƙaramar hukumar Jibia, wanda makarantar ta samu gagarumin sauye-sauye a ƙarƙashin jagorancinsa.

Taron dai na da nasaba da zaburar da sauran ɗalibai da za su ci gajiyar haddar Al-Qur’ani maigirma da samun ɗaukaka da ƙima a idon Duniya da kuma Addinin Musulunci.

~katsina post









Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button