Labarai

Zargin maɗigo: Kotu ta Aike Da Ramlatu Zuwa Gidan Gyaran Hali

Advertisment

Kotun shari’ar Muslunci da ke Hisbah a jihar Kano, karkashin jagorancin mai shari’a Sani Tanimu Hausawa, ta yanke hukuncin dauri a gidan yari na wata bakwai da zaɓin tarar N50,000 ga matashiyar ’yar TikTok, Ramlat Muhammad.

Tunda fari Hisbah ta gurfanar da matashiyar ne bisa tuhume-tuhumen fitsara da rashin tarbiyya da yada ɓaɗala, yawon banza da ta zubar sai kuma fitsara wanda ya saba da sashe na 385.

A tuhumar farko alkalin ya yanke wa Ramlat hukuncin zaman gidan yari na tsawon wata uku ko zabin tara ta Naira dubu talatin.

Sai laifin yawon banza, wanda a kansa alkalin ya yanke mata hukuncin daurin wata uku a ko zabin tara na Naira 20,000.

A laifi na uku da aka kama ta da shi na fitsara kuma alkalin ya yanke mata hukunci bisa sassauci da ta nema zaman gidan yari na tsawon wata guda babu zabin tara.

Wani Labari : Tun ranar Alhamis mu ka saki Murja bisa umarnin kotu – inji kakakin gidan yari

Kakakin gidan gyaran hali na jihar Kano AC Misbahu Kofar Nassarawa ya shaidawa DAILY NIGERIAN cewa sananniyar ‘yar Tiktok Murja Kunya ba guduwa ta yi daga gidan yari ba.

A cewar sa, tun ranar Alhamis takarda ta zo daga kotu don neman a sake ta, kuma gidan yarin ya sake ta a ranar.

Ya ƙara da cewa kotu ce ta kawo ta ajiya a wajensu, kuma kotu ce ta ce su sake ta.

Advertisment






Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button