Labarai

Za’a iya ɗaure Ramlat Princess Har Na tsawon Shekara Goma Sha huɗu

Advertisment

Wata yarinya yar tiktok mai suna Ramlat princess tayi bidiyo a manhajar tiktok tana mai cewa ita fah idan har mutum zai aure ta sai anyi yarjejeniya ya samo mata abokiyar zama wata yar madigo idan bai aminta ba bazata aminta ba.

A daren jiya hukumar hisbah karkashin kwamandan Sheikh Aminu Ibrahim daurawa sunyi nasarar cafke wannan yarinya kamar yadda sunka fadi a shafinsu na facebook mai suna mujallar hisbah kano.

Shine masanin Shari’a barista Shehu Rahinat Na’Allah ya fadi irin hukucin da za’a iya yiwa wannan matashiyar yarinyar akan dokar kasa.

“Maɗigo“ da Hausa ko “Lesbian“ da turanci Ko Kuma “Sihâƙ“ da larabci, haramun ne a dokar Allah kai Har ma da dokar ƙasa, kazalika Koda Babu dokar Allah Ko ta ƙasa to Duk Wani “Aƙlus-Saleem“ Zai tabbatar ma da maishi cewa wannan ɗabi’a ta Lesbian ba Mai Kyau bace.

Advertisment
Za'a iya ɗaure Ramlat Princess Har Na tsawon Shekara Goma Sha huɗu
Za’a iya ɗaure Ramlat Princess Har Na tsawon Shekara Goma Sha huɗu Hoto: facebook/ mujallar hisbah kano

Akwai ƙasashen Duniya da Dama waɗanda Suka haramta wannan baƙar ɗabi’a Kuma Suka tanadi hukunci Mai tsanani akan duk Wanda aka sameshi Yana aikata ta, Wanda ita ma ƙasar mu Nigeria tana Cikin Jerin ƙasashen da Suka haramta. A shekarar 2013 lokacin Dr. Goodluck Ebele Jonathan Yana Shugaban ƙasa, Majalisa tayi Wani kundin doka Mai Suna “Same Sex Marriage (Prohibition) Act, 2013“ Wanda ya haramta yin auren Jinsi ta Kowanne ɓangare, bama auren kaɗai ba Har da yin Soyayya a tsakanin Jinsi ɗaya Ko Kuma Duk Wani abu da yake alamta Soyayya tsakanin Jinsin Kamar yadda yazo a Sashi Na 1, 2, 6 dana 7 na Same Sex Marriage Prohibition Act, 2013.

Don haka, Duk Wanda aka sameshi da aikata wannan laifin Zai fuskanci ɗauri a Gidan gyaran Hali Har Na tsawon Shekara Goma Sha huɗu Kamar yadda yazo a Sashi Na 5(1) Na Same Sex Marriage Prohibition Act, 2013. Sannan Duk Wanda ya halarci ɗaurin auren Ko yaje wurin bikin auren, Ko ya taimaka, Ko ya bada goyon Baya, Ko ya Shaida, Ko ya bada Shawara, to ya aikata laifin da za’a ɗaure Shi Na tsawon Shekara Goma Kamar yadda Sashi Na 5 (2) ya tabbatar. Sannan Sashi Na 6 ya tabbatar da cewa Babbar kotun Jiha (State High Court) Ko ta tarayya (Federal High Court) su kaɗai ne suke da hurumin Sauraren wannan ƙarar, saboda haka kotun Musulunci Ko Magistrate court ba suda hurumin Sauraren wannan ƙarar.

Don haka, idan Har laifin ya tabbata to za’a iya ɗaure ta Har Na tsawon Shekara Goma Sha huɗu a Gidan Gyaran Hali.

Advertisment








Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Advertisment
Back to top button