Labarai

Turkiyya ta kama mutum 7 da ake zargi ‘yan leken asirin Isra’ila ne

Hukumar leken asirin Turkiyya (MIT) tare da hadin gwiwar ofishin babban daraktan tsaron kasar sun yi nasara a wani samame da suka gudanar kan wasu da ake zargi da alaka da hukumar leken asirin Mossad ta Isra’ila.

Jami’an tsaron sun gudanar da samamen ne a Istanbul da Izmir, inda suka yi nasarar cafke mutum bakwai da ake zargi da bayar da bayanai a fakaice ga Mossad, kamar yadda majiyoyin tsaro suka bayyana a ranar Juma’a.

 

Jaridar TRTAFRIKA Hausa na ruwaito cewa, tun da fari a aikin binciken, ‘yan sanda sun kama mutane biyu daga cikin mutum tara da ake nema ruwa-a-jallo, kafin sauran su shiga hannu, a cewar bayanan.

Turkiyya ta kama mutum 7 da ake zargi 'yan leken asirin Isra'ila ne
Turkiyya ta kama mutum 7 da ake zargi ‘yan leken asirin Isra’ila ne

Binciken ya nuna cewa Mossad na yin amfani da jami’an leken asiri masu zaman kansu don bin diddigin mutanen da take son kai wa hari a Turkiyya.

 

Hukumar leken asirin Isra’ila kan yi amfani da ‘yan leken asiri masu zaman kansu wajen samun bayananta kamar tattara bayanan tarihin rayuwar mutum da kuma aikin sa ido da bincike da tattara hotuna da bidiyoyi da bibiya kai-tsaye da kuma kutse a na’urorinsu.

 

A ci gaba da binciken da ofishin babban mai shigar da kara na Istanbul ya gudanar ya gano wasu mutane tara da ke da alaka da hukumar leken asirin Isra’ila.

 

An gano wadannan mutanen suna sayar da bayanai ga Mossad don samun kudi.

 

Wannan samamen na nuna gagarumar nasarar da Turikyya ta samu kan hukumar leken asirin Isra’ila ta Mossad, bayan gudanar da makamancinsa a watan Disamba na 2023, inda aka gurfanar da mutane 68 a kotu.

Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button