Tsadar Rayuwa: Najeriya Na Iya Fadawa Cikin Rikici —AfDB
Bankin Raya Afirka (AfDB) ya yi gargadin cewa tsadar rayuwa da ake fama da ita a Najeriya na iya haddasa barkewar rikici a kasar.
AfDB ya yi gargadin ne a cikin rahotonsa na tattalin arziki da kuma hasashen shekarar 2024 inda ya yi hasashen tattalin arzikin nahiyar Afirka zai karu sama da kashi 3.2 cikin 100 da aka samu a shekarar 2023.
’Yan Najeriya a jihohin Kano da Neja da Legas da sauransu sun gudanar da zanga-zangar nuna adawa da tsadar rayuwa da ake fama da ita a kasar.
A ranar Labara, Sarkin Musulmi kuma Shugaban Majalisar Sarakunan Arewa, Muhammad Sa’ad Abubakar, ya shaida wa wani zaman da suka yi a Kaduna cewa miliyoyin matasan da ke zaune babu aikin yi babban hatsari ne ga kasar.
Jaridar Aminiya na ruwaito, kafin nan, a ranar Litinin, Sarkin Kano, Aminu Ado Bayero, ya bayyana cewa ’yan Najeriya na cikin wahala sosai, inda ya bukaci uwargidan shugaban kasa, Sanata Oluremi Tinubu —wadda ta ziyarci fadarsa — da ta isar da sakon ga mijinta domin a dauki matakin da ya dace.
A ranar Labarabar, Ministan Noma da Samar da Abinci, Abubakar Kyari, ya ba wa ’yan Najeriya tabbacin gwamnati za ta raba metric ton 42,000 na hatsi kyauta.
A ranar Juma’a dai Kungiyar Kwadago ta Najeriya (NLC) ta ayyana zanga-zangar kwanaki biyu a fadin kasar a ranakun 27 da 28 ga watan Fabrairu.
Shugaban NLC, Joe Ajaero, ya ce sun dauki matakin ne bayan cikar wa’adin kwanaki 14 da suka bai wa gwamnati na magance wahalhalun da ake sha a kasar.
A karshen mako AfDB ya yi gargadin cewa rikice-rikicen cikin gida na iya tasowa a sakamakon karin kudin wutar lantarki da na kayan masarufi baya ga faduwar darajar Naira da cire tallafin makamashi a kasashen Najeriya, Angola, Kenya da Habasha.
~Aminiya