Takaitaccen tarihin Fatima Hussaini Abbas “Maryam Labarina”
Fitacciyar jarumar masana’atar Kannywood maryam labarina ta bada kadan daga cikin takaitaccen tarihin rayuwar ta zuwa yanzu da gidan jaridar TRTAFRIKA Hausa nayi fira da ita.
Ga kadan daga cikin takaitaccen tarihin Fatima hussaini Abbas wanda anka fi sani da labarina.
Fatima hussaini Abbas abbas shekaruna 23 an haifi ne an haifi ni ne a jos a jihar filato, na taso a abuja har na kai aji biyu a firamare , Sa’a nan kuma koma garin kaduna, na fara da aji biyu har na gama, na gama makarantar sakandare.
Na yi karatun IJMB duk a kaduna, kafin na fara karatun diploma yanzu haka ina a karatun babbar diploma (HND) a fannin SLT a kwalejin kimiyya da fasaha ta nuhu bamalli “polytechnic” da ke zaria .
Taya kin ka tsinci kanki a kannywood ?
Kamar yadda na sha fadawa kawaye na cewa kowa zai iya taya rawa a harka fim, domin daman ina da sha’awar harka sai Allah yasa ashe ina da rabo na samu.
Wace irin matsala kinka fuskanta shigowar ki kannywood?
“Gaskiya da na shigo kannywood na fuskanci kalubale kadan saboda da gaskiya da waka na fara , ina waka haka sannan ina rubuta jifa jifa da na je bebeji suna sai flex T ya kira ni, wanda shima mun hada shi ne ta harkar waka ne ina son daukar waka sai yace min su mazaje zasu dauki wata waka.
Ta wani fim mai suna jinin masoya, kuma ana so na shiga da na zo naga labari baiyi ba sosai, kuma ‘yan wasa muna yin tunani bayan mun ga labari ko zai mana ki bazai mana ba, sai naga bai yi min ba,sai nayi magana da mazaje nace ina da labari.
Ga yadda labarin yake sunan labarin nikab sai ya ce yana son labarin , sai ya ce daga yau sunan labarin sirrin kyau, sai ya dauki nauyi fim din sirrin kyau Usi madobi ya taya ni wajen rubuta labarin fim din.
Shin shirin labarina shine shirinki na Farko?
A’a ba labarina ba ne fim dina na farko ba, kafin labarina ina da finafinai kusan biyar ina da na ladidi,sirrin kyau, fatake, amarya, makarantar farko da sauransu.
Mene ne ya sauya bayan fitowarki a cikin labarina ?
Gaskiya bayan fitowar labarina kalubalin da na fuskanta ita ce wasu shafukan sada zumunta , saboda ba zan ce gaba ba wasunsu suna kokarin batamin bata ni da bude shafin bogi da sunana, suna yada abun da bai dace ce ba, akwai wani bidiyo fa da wata yarinya take rawa, tana sanye da wasu kaya da ke bayyana tsirancinta tana rawa.
Zan iya cewa ko don saboda doguwa ce baka masu yada abubuwa a shafukan sada zumunta , sun ga bidiyon sun san cewa bani ba ni ba ce, amma suna kokarin batar da mutane akan cewa ni ce a wannan bidiyon.
A rinka kalamai game da bidiyon marasa daɗi , amma ban ga laifin su masu yin kalamai ba, zan iya cewa nayi musu uzuri na yafe musu, amma dan Allah kafin su yanke min hukunci a kan abu su tabbatar da cewa abu ne sahihi su kuma masu yadawa a shafuka ku yi hakuri ku daina yada abin da shi ne ba.
Haka zalika akwai wani bidiyo da munkayi ni da wani ɗan uwana da munkayi shi Shekara hudu da suka wuce a shekarar 2020 muna dan nishadi ne a lokacin muka yi wannan bidiyon wanda ni na manta da bidiyon gaba daya , sai aka samu wasu sun aje bidiyon sun rasa lokacin da za su fito da shi sai yanzu , ga ni bidiyon bai kunshi wani abu mara kyau ba, amma ga wadanda ba su ji dadinsa ba, zan iya cewa shima suyi hakuri, ina ganin saboda mun a wurare daban daban ne, amma kuyi hakuri dan uwana ne, uwarmu daya ubanmu daya shine ma ke bina gaskiya.