Labarai

Ramin da muke ciki a yanzu, a lokacin Buhari aka haka shi – Dr. Hakeem Baba-Ahmed

Yau dai ina jin sha’awar magana ne da wadanda ke kalamai da ke nuna fushi ko suyi batanci saboda ba su ji na ina magana game da Arewa ko yanayin kasa ko shugabanci ko wahalar rayuwar talaka a wannan zamani.

Kamar yadda aka sani dai, ina aiki a ofishin Shugaban Kasa da Mataimakin sa a matsayin mai bada shawara a fannin siyasa. Abin da mutane da yawa basu sani ba shine rayuwa ta kaf na yi ta ne cikin aikin gwamnati da koyarwa.Na rike mukamai iri iri, Alhamdilillah, kuma na gode wa Allah na gama lafiya.Na yi aiki har shekara goma a matsayin Permanent Secretary a Federal Government, bayan na yi Perm Sec a jiha ta ta Kaduna, na yi SSG, na yi Chief of Staff na Senate President, da ayyuka da yawa na yi wa kasa hidima. Saboda haka, ni mukami ba wani abu ne sabo a wuri na ba. Allah Ya rufa mani asiri na koma pansho, na kuma koma inda na fara, watau malanta. Abin da nike samu ta wadannan hanyoyi, na gode wa Allah, ya raba ni da kwadayin mukami ko wulakanta kai na.

Ina sane, mafi yawan masu zargin kwadayin mukami ya kai ni wannan matsayi da nike rike da shi yanzu ba su san ma ko ni wanene ba, kafin su ji ni ina fafitikar kare Arewa da talaka. Tarbiyyar da iyayen mu suka yi mana shine mu bauta wa Allah, mu kuma tsayawa gaskiya a cikin ko wane hali muke. Mutane da yawa sun sanni ne a matsayin mai magana da yawum Kungiyar Dattawar Arewa ( Northern Elders Forum), wacce tayi fice wajen kare mutumcin dan Arewa a Nigeria. Da yawa daga cikin mu a wannan kungiyar, mun shigeta ne saboda mun ga manyan mu su ma suna kare Arewa.Tun muna daukan masu kaya, har Allah Ya bamu masu daukan mana kaya mu ma. Na gode wa Allah da ya bani dama in yi Arewa da kasata hidima da har wasu da yawa za su shede ni da shi.

An nemi ni in zo in taimaka a gyara barnar da a ka yi wa kasa da talaka cikin shekarun da suka wuce. Na yi juyayin amfanin da zan yi idan na karbi aikin da aka ce na zo na yi. Na roki Allah Ya nuna man abin da zai fi alheri.Na yi shawara. A karshe, na tsai da shawarar amsa gaiyata na shiga hidimar tada gini, maimakon kururuwar rushen ginin da ya fado mana mu duka. Na san zan bar gurbi, amma na roki Allah Ya bada wanda zai maye gurbin, ko ma ya fi ni kokari.

Aikin da nake yi yana da amfani, musanman ga mu ‘yan Arewa, amma ba na yi ana hayaniya ba ne. Barnar da aka yi wa kasa, balle ma Arewa,a karkashin shugaba daga Arewa tana da yawa.Ramin da muke ciki a yanzu, a lokacin Buhari aka haka shi. Wannan gwamnnatin tana bukatan wadanda suka nakalci shirin fita daga cikin mummunan halin da muke ciki.Duk kuwa wanda yace akwai maganin da za’a iya yi mu fita daga mummunan halin da muke ciki cikin takaitaccen lokaci, ko akwai yadda za’a dora karaya ba’a ji zafi ba, karya yake. Gaskiya daci gareta, amma karya cuta ce.
Talaka kam yana shan wuya, kuma kullum sai an tambaye ni ko me nake cikin gwamnatin da ke wahalar da talaka. Ni na sani, tsakani na da Ubangijin da zai man hukunci, akwai amfanin da nike yi.Duk ranrar da kuma naga bani da wani amfani a wajen neman gyara, to kafar da ta kawo ni ita zata fitar da ni, in sha Allah.

Wadanda ke cin mani zarafi saboda iyakar siyasar da suka sani ke nan,sai suyi ta yi.Na yafe masu, har lahira.Masu nuna masu wannan ita ce siyasa sun kware su. Zagin manya ba alheri ba ne, kuma kowa na da babba, ko kuma kila zai zama babba.
Wadanda ke jin zafin Arewa ta rasa daya daga cikin masu mata hidima, sai su yi hakuri.A inda nake ma Arewar nake wa hidima.

Wadanda suke cewa babu dattijai a Arewa su yi hattara. Lokacin da muka tsaya wa Arewa, mu ba dattijai bane? A daina zagin dattijai, domin ko a gida akwai su.
Wadanda ke cewa el-Rufai ya ce babu dattawa a Arewa, to sai su je su kawo shi ya nuna yadda ake dattaku a Arewa, amma ya fara da yadda ya tafiyar da Kaduna.
Wadanda ke gadon gaba basu san hujja ko dalili ba, su yi tambaya. Idan da Dr Hakeem dattijon banza ne, me zai sa a yi ta kewar sa haka? Arewa tayi dattawan kirki har mutuwar su. Allah Ya sa karken mu ya yi kyau.

Ina barar addu’a, Allah Ya idar mani da niyya ta ta shiga wannan aikin. Ina rokon mu mu duka mu binciki kan mu.Ina imanin mu da tarbiyar mu ta ‘yan Arewa? Mu taimakawa juna da kyawawan zato, kuma mu taimaki kan mu. Idan Allh Ya kai mu wani zaben, mu daure mu zabi mutane masu tsoron Allah, masu tausayi, wadanda suka san abin da zasu yi da mulki ba cika aljihun su da dukiyar talakawa ba. Akwai aiki ja a gaban mutanen Arewa. Bata wadanda ke son gyara ba alheri ba ne.Mu ji tsoron ranar da zamu tashi babu mai son ya gyara domin yana tsoron zagin wadanda suke cikin ukuba.

Allah Ka shirye mu, Ka kawo mana karshen wannan irin iftila’i da muke ciki.
Na gode.

Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button
DOMIN SAMUN GARABASA