Labarai

RAƊAƊIN TSADAR RAYUWA: ‘Ba Najeriya kaɗai ke fama da tsadar rayuwa ba, Amurka da Ingila ma sun shiga tasku’ – Barau Jibrin

Sanata Barau Jibrin ya bayyana cewa halin tsadar rayuwa da tsadar kayan abinci da ake fama da shi a Najeriya, ba nan kaɗai abin ya shafa ba.

Barau wanda shi ne Mataimakin Shugaban Majalisar Dattawa, kuma Sanata mai wakiltar Kano ta Arewa, ya ce yanzu haka ita ma ƙasar Ingila ta afka taskun matsin tattalin arziki, haka ita ma Amurka da sauran ƙasashen duniya.

Jibrin ya ce yadda Najeriya ke fama da tsadar abinci, haka ƙasashen duniya da dama.

Premium Times Hausa na ruwaito cewa,Jibrin ya danganta mummunan al’amarin da dalilai da dama, ciki har da yaƙin Ukraniya da Rasha, wanda ya haifar da ƙarancin abinci a duniya.

Shi kuwa Sanata Akpabio iƙirari ya yi cewa ‘kowane gwamna ya karɓi Naira biliyan 30 daga Tarayya, domin raba wa talakawa abinci’.

Shugaban Majalisar Dattawa, Godswill Akpabio, ya yi iƙirarin cewa ya samu labarin da bai tabbatar ba cewa Gwamnatin Tarayya ta bai wa kowane gwamna kuɗin kishi-kishi, har kowa ya karɓi Naira biliyan 30, domin su rage wa talakawa raɗaɗin tsadar rayuwa.

Akpabio ya bayyana cewa an ciri kuɗin ne daga Asusun Gwamnatin Tarayya an raba wa gwamnonin domin a rage tsadar kayan abinci da tsadar rayuwa a kowane jiha.

RAƊAƊIN TSADAR RAYUWA: ‘Ba Najeriya kaɗai ke fama da tsadar rayuwa ba, Amurka da Ingila ma sun shiga tasku’ – Barau Jibrin
Jibrin Barau

Akpabio ya bayyana haka a zaman Majalisar Dattawa na ranar Talata, inda ya ce labarin da ya zo masa na nuni da cewa an ba su kason farko ba tun yau ba, sannan kuma gwamnonin dai sun sake karɓar Naira biliyan 30 kowanen su daga Hukumar Tara Kuɗaɗen Haraji ta Ƙasa (FIRS).

“Tilas ta kama zan bayyana cewa kowace jiha ta karɓi Naira biliyan 30 cikin ‘yan watannin nan daga Hukumar Tara Kuɗaɗen Haraji ta Ƙasa (FIRS).

“Waɗannan kuɗaɗe da aka ba su, ba su cikin haƙƙin kuɗaɗen su da gwamnatin tarayya ke ba su na duk ƙarshen wata daga Asusun Gwamnatin Tarayya. An ba su ne domin su rage wa talakawa raɗaɗin tsadar rayuwa da tsadar kayan abinci,” cewar Akpabio.

Akpabio ya shawarci gwamnoni su yi amfani da kuɗaɗen ta inda ya dace, kuma ta hanyar amfana su ga talakawa da marasa galihu, domin rage masu tsadar rayuwa.

“Mun yi amanna da cewa matsawar gwamnoni za su yi amfani da kuɗaɗen ta hanyar wadatar da abinci, to za a samu sauƙi sosai.

“Gwamnatin jiha na da jan aiki a kan ta. Ita ce kusa da jama’a. Ba na so na ce ƙananan hukumomi ne suka fi kusanci da jama’a, domin kowace ƙaramar hukuma a yanzu ƙarƙashin gwamna take.

“Amma dai na yi amanna cewa idan gwamnatin jiha za ta yi abin da ya kamata, to sai ta jawo ƙananan hukumomi wajen raba kayan abincin ga mabuƙata.” Inji Akpabio.

~ Premium Times Hausa

Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button