Najeriya a damalmalalle ta ke, ta na buƙatar ƙaƙƙarfan garambawul – Ango Abdullahi
Shugaban Ƙungiyar Dattawan Arewa, Ango Abdullahi, ya bayyana cewa tsarin da Najeriya ke a kai yanzu ya hargitse, kuma a damalmale ya ke.
Dangane da halin da ya ce ƙasar ke ciki, ya bada shawarar a yi wa Najeriya ƙaƙƙarfan garambawul.
Farfesa Abdullahi, wanda tsohon Shugaban Jami’ar Ahmadu Bello ta Zariya ne, yayin da ya ke jawabi a wurin ƙaddamar da littafi mai suna “Court and Politics”, Wanda Umar Arɗo ya wallafa, a Abuja.
A taron wanda aka gudanar ranar Asabar, Ango Abdullahi ya ce, “ganin halin da ƙasar nan ke ciki, zan iya cewa shugabani da waɗanda ake mulka sun gaza wajen samar da nagartacciyar ƙasa.
“Wannan taro ni a gani na wata dama ce gare mu domin mu yi wa kan mu faɗa cewa mu duka ke da laifi.
“Yanzu ɗin nan aka ɗauke wuta. Har yanzu tsawon shekaru 64 mun kasa samun wuta fiye da shekaru 64, wadda muke amfani da ita ba ta wuce migawat 4,000 ba. Wannan ai babban abin kunya ne.
“A wata ƙasar wuta mai ƙarfin migawat 4,000 ba za ta wadaci wani babban gidan ɗaya ba.
“Waɗanda a cikin mu ke zuwa Saudiyya aikin Hajji daga lokaci zuwa lokaci, zan tunatar da ku cewa wutar lantarkin da ake amfani da iya a Masallacin Ka’aba ta kai migawat 18,000 a kullum.
“Mu kuma nan a Najeriya, ƙasa mai al’umma miliyan 220 muna samun migawat 4,000, bayan shekaru 64 da samun ‘yanci.
“Maganar gaskiya wannan laifin kowa ne, tun daga masu mulki da waɗanda ake mulka, ” inji Abdullahi.
Ango Abdullahi ya yi kira a koma tsohon tsarin shugabanci na Firayi Minista, maimakon na shugaban ƙasa wanda ake kai a yanzu.
Ya ce tsarin shugaban ƙasa ya na haifar da kashe maƙudan kuɗaɗe a dimbin wurare da hanyoyin da ba su dace ba.