Labarai

Na fitar da kuɗin dala miliyan 6.2 da sa-hannun bogi na buhari

Tsohon sakataren gwamnatin tarayya ya bayyana cewa an kwaikwayi tadda tsohon shugaban Kasa Muhammadu Buhari da shi kansa ne aka cire dala miliya 6.2 daga asusun babban bankin Najeriya batare da sun sani ba.

Mustapha ya ce maida martani ne bayan an zarge shi da shugaba Buhari da hannu dumu-dumu a harkallar cire kudi har dala miliyan 6.2 dominwai biyan masu kula da zabe.

Premium Times Hausa na ruwaito cewa,Mustapha ya bayar da shaida ne a ci gaba da tuhumar Godwin Emefiele, tsohon gwamnan babban bankin kasa CBN, a kotu a Abuja.

Mustapha ya bayyana a kotu cewa lallai an kwaikwayi yadda suke saka hannu ne shi da shugaba Buhari ba tare da sun sani ba, aka fidda wadannan kudade daga babban bankin Najeriya CBN amma ba bu ruwan sa sannan babu sa bakin Buhari

” Ya maishari;a an yi taro kuma shi ne taro na farko, ba 187 ba kamar yadda suka ce ba. Shi ne taron farko na shekara. Ya Ya maishari’a, duk tarukan FEC shugaban kasa ne ko mataimakin shugaban kasa ne ke jagoranta. A ranar 18 ga watan Janairu, mataimakin shugaban kasa ne ya jagoranci taron saboda shugaban ba ya kusa. Aikina shi ne na shirya ajandar taron kuma a wannan rana akwai ajanda guda 16, kuma babu ajanda da ta shafi masu sa ido na kasashen waje, don haka bai bayyana a FEC na 18 ga Janairu ba, babu irin wannan amincewa da aka yi a wannan rana.

” Ya maishari’a, ina so in tabbatar maka cewa a iya tsawon aiki na a matsayin sakataren gwamnatin tarayya, ban taba cin karo da wannan takarda ba da ke wai har yana dauke da saka hannu na da na tsohon shugaban kasa Buhari ba. Kaga sa hannun mu aka yi aka cire kudaden daga CBN.

SHARI’AR RANAR FARKO: Mai bayar da shaidar da mai gabatar da ƙara ya gabatar wa Babbar Kotun FCT Abuja, ya bayyana wa Mai Shari’a gwamnatin tsohon Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari ta bada umarni aka kamfaci Naira biliyan 2 da Naira miliyan 900 domin biyan masu sa-ido kan zaɓen 2023.

Wanda ta bada wannan shaida ita ce Onyeka Ogau, tsohuwar Mai Kula da Reshen CBN, wadda ta yi wannan bayani a lokacin da ta ke bada shaida a shari’ar da ake ci gaba da gudanarwa ta tuhumar tsohon Gwamnan CBN, Godwin Emefiele.

Ogau ta ce ta karɓi umarnin ta biya Dala miliyan 6.23 a ranar 8 ga Janairu, 2023, kamar yadda wani bayanin da Hukumar EFCC ta fitar, wanda ya labarta yadda zaman kotun ya wakana a ranar Litinin.

Mai bayar da shaidar dai lauyan EFCC ne ya gabatar da shi, wato lauya Oyedepo Rotimi, SAN a gaban Mai Shari’a Hamza Muazu.

Ogau ta ci gaba da yi wa kotu bayanin cewa an rubuto masa takardar umarni daga na gaba da shi, wadda a Turance ake kira ‘memo’, an haɗa takardar da kwafen bada umarnin cirar kuɗaɗen da Shugaba Muhammadu Buhari, Sakataren Gwamnatin Tarayya, Boss Mustapha da kuma Godwin Emefiele.

Ɗaya daga cikin umarnin ya ce a biya Dala miliyan 6.23 ga wani ma’aikacin Ofishin Sakataren Gwamnatin Tarayya.

An cire kuɗaɗen cikin Janairu, 2023, lokacin farashin Dala 1 a hannun Gwamnatin Tarayya Naira 461 ce. Hakan ya nuna an cire adadin Naira biliyan 2.9 kenan.

– Premium Times Hausa

Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button