Muna goyon bayan a raba kasar Nijeriya – shugaban gamayyar kungiyoyin matasan arewa
Shugaban ƙungiyar gamayyar kungiyoyin matasan arewa Ashiru shariff Natsura yayin da yake tattaunawa da manema labarai ya jadda goyon bayan su da zauna a raba kasar nan Nijeriya kowa ya kama gabansa.
Ashir shariff Natsura ya kawo misalin cewa a lokacin da ankayi end sars aka kona tirela kusan sittin da wani abu, inda irin yan arewa sunyi irin wannan sun janye kai kayan abincin anzo an tsaya anyi maganganu da yanzu an biya su diyar abubuwan da ankayi musu na ɓarna na rayuka da dukiyar su anka ƙi yi.
Mufa yanzu abinda muka so kowa ya gane a Nijeriya mufa ba dole sai anyi zaman kasar nan daya ba, mu bai dame mu ba, shiyasa tun ainayi kakanmu da ya gina arewancin Nijeriya sir. Ahmadu Bello Sardauna tun ainahi yace wannan zalunci ne, kuskure ne hada kudancin nijeriya da arewan Nijeriya a matsayin kasa mu bamu goyi bayansa ba.
Mu a zo a raba kasar nan lami lafiya kowa ya kama gabansa, ba sai anyi amfanin da yaƙe-yaƙe da tashin hankali kafin a raba kasa ba.
Mu muna goyon bayan azo a zauna a duba kadarorin kasar nan a raba ko wane yanki a bashi nashi hakinsa, a bashi a raba kasa cikin kwanciyar hankali , ba tare da sai anyi tashin hankali ba.
Bugu da kari ashir shariff ya kara da cewa kuma mun sha fadar wannan maganar bazamu yarda ace wai ta’allaka Nijeriya da zubada jinin da duniya idan ana so Nijeriya ta zamo kasa , shi mutumin arewa ya hakuri ransa ba a bakin komai ba, dukiya da jininsa da rayuwar sa ba’a bakin komai ba.
Ba wanda zai dora muna wannan abun mu yarda ba’a isa ba kowa ye shi , gara a raba kasar kowa ya kama gabansa yaje yaga abinda zaiwa kasa, amma zamu yarda a kashe mutumin arewa ba yayi hakuri a kone dukiyarsa aci mutucinsa sa’a nan Nijeriya zata rayu a matsayin kasa ba, bazamu taɓa yarda da wannan abun ba kuma bamu goyi baya ba.- inji Ashir shariff Natsura