Labarai

Matawalle Yayi Allah-Wadai Da Kalaman Dattawan Katsina Kan Cewa Ba Zasu Zaɓi Tinubu A 2027

Advertisment

Tsohon gwamnan jihar Zamfara kuma ƙaramin ministan tsaro na Najeriya, Bello Mohammed Matawalle ya yi watsi da kalaman ƙungiyar dattawan jihar katsina a kan sake zaɓen Shugaba Bola Ahmed Tinubu a 2027 da cewa ba ra’ayin al’ummar arewacin Najeriya ba ne.

Ministan na martani ne a kan barazanar da kungiyar dattawan (Katsina Elders’ Forum) ta yi ne a kan shugaban ƙasar a kan matakin gwamnatinsa na mayar da hukumar kula da filayen jirgin sama na ƙasar da aikin faɗaɗa filin jirgin sama na Umaru Musa Yar’Adua da ke Katsina da kuma wasu sassan babban bankin kasar daga Abuja zuwa Lagos.

Wasu rahotanni da dama na cewa kungiyar dattawan ta buƙaci shugaban ƙasar da ya sauya shawara a kan wannan mataki da ya ɗauka ko kuma ya rasa goyon bayan al’ummar arewacin ƙasar a zaɓen 2027.

Matawallen Maradun ya bayyana barazanar ƙungiyar ta Dattawan na Katsina da cewa ba komai ba ne illa wani yunƙuri na haddasa ƙiyayya da tsana da raba kai da kuma neman haddasa fitina tsakanin arewacin najeriya da ‘yan uwansu na sauran sassan ƙasar.

Advertisment
Matawalle Yayi Allah-Wadai Da Kalaman Dattawan Katsina Kan Cewa Ba Zasu Zaɓi Tinubu A 2027
Matawalle

Ministan ya ce bai dace ba a ce dattawan sun yi waɗannan kalamai a madadin arewacin Najeriya duk da cewa sun sani sarai cewa ba ra’ayin yawancin al’ummar arewa ba ne

Katsina Reporters sun ruwaito cewa tsohon gwamnan na zamfara ya ce abin da arewacin Najeriya ke buƙata a yanzu shi ne tsaro ga rayuka da dukiyarsu, abin da ya ce Shugaba Tinubu ya duƙufa samarwa.

Ƙaramin ministan tsaron ya kuma yi barazanar cewa gwamnati ba za ta lamunci duk wani abu da zai haifar da naƙasu ga dumukuraɗiyyar ƙasar da kuma haddasa ƙiyayya tsakanin arewa da sauran sassan ƙasar ba.

Advertisment








Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Advertisment
Back to top button