Matan Aure A Fatakwal Sun Yi Zanga-zanga Saboda Ƙarancin Samun Jima’i Daga Mazajen su


Allah ɗaya gari bamban yayin da mata masu sana’ar gurasa a jihar Kano suka yi zanga-zanga sakamakon tsadar fulawa. Su kuma mata ne a garin Fatakwal suka yi zanga-zanga saboda ba sa samun yawan jima’i daga Mazansu. Sarauniya news na ruwaito
Fustattun matan da suka fito daga mil 2 da kuma mil 3 na unguwar Diobu a garin Fatakwal sun yi dafifi zuwa ofishin samar da lantarki tare da korafin ƙarancin wutar lantarki da ake fama da shi a ƙasa ta janyo mazansu na kauracewa shimfiɗarsu saboda tsananin zafi da baya bari su yi barci.
A yayin da ake zuba tsananin sanyi a Arewacin Najeriya su kuma Kudancin ƙasar tsananin zafi ake zubawa.
Wani Labari : An aikewa majalisar dokoki takardar neman rushe Masarautu hudu da dawo da Sunusi Sarkin Kano
Yanzu haka wata kungiya mai suna “Yan Dangwalen Jihar Kano” ta rubutawa majalisar dokokin jihar Kano takardar neman rushe dokar kafa karin masarautu hudu da suka hadar da Gaya, Rano, Karaye da Bichi, wadanda gwamnatin da ta gabata ta kafa, tare da neman a maido da Sarkin Kano na 14 Mallam Muhammadu Sanusi II.
Dala fm na ruwaito,bayanin kungiyar na zuwa ne ta cikin wata wasika mai kwanan watan Fabrairu 5, 2024, da aike wa kakakin majalisar dokokin jihar Kano, inda ta ce rusa masarautu tare da maido da Muhammadu Sanusi na biyu a matsayin sarkin Kano “zai samar da hadin kai, zaman lafiya da kwanciyar hankali a fadin jihar Kano.