Manyan Laifuka Bakwai Da Ake Zargin Murja kunya Da Aikatawa – Sheikh Ibrahim Daurawa


As-sheikh Aminu Ibrahim daurawa ya bayyanawa gidan jaridar Dw hausa cewa suna tuhumar murja kunya manyan laifuka guda bakwai 7 da ta aikata har sunka kama ta domin gurfarar da ita.
Sakamakon korafe korafen ake tayi akanta wanda har anka shirya tuhumomi guda bakwai 7 akanta, daman idan baka manta ba mun taba kiran su munkayi musu nasiha munka basu shawarwari, munkayi musu wa’azi munkayi musu addu’a har muka dan kawo kuɗi haka munka basu na sayen data, mun kace suje su juya harka tiktok zuwa sana’a da kasuwanci da talla.
Su daina yin kalamai na batsa da abubuwa da basu dace ba wanda suka lalata tarbiyya, sunkayi muna alkawali musamman ma ita tayi mana alkawali cewa bazata sake irin yin abubuwa ba, saboda haka sai kuma gashi yanzu ana ta samun korafi abubuwa sunyi yawa, musamman mutanen unguwar da take zaune cikin shama su turomana cewa tana lalata musu tarbiyyar yara, harma akwai bazarana da su ke kanta, shiyasa ita hukumar hisbah taga bari ta kamota ta kaita kotu sai kuma abinda alkali yace.
Kamar waɗannan irin tuhume-tuhume ne ake akanta?
To an karanta wadannan tuhumi a kotu , kuma ta mu sa waɗannan tuhumomin guda bakwai dan haka shiysa alkali ya tura ta gidan gyaran hali sai ranar ashirin da bakwai ga watan biyu za’a dawo a cigaba da shari’ar.
Daga cikin tuhumar da ake mata akwai:-
Razana al’umma
Ayyukan baɗala
Tada hatsaniya
Tada hankalin al’umma
Ta’addanci da kawo ɓata gari cikin unguwa.
Ikirarin cewa duk wata karuwa ko ƴar kwalta itace shugabar su.
To wadanda abubuwa suna tada hankalin mutane, kuma duka wadannan abubuwa akwai hotuna da bidiyo da duk abubuwan din nan da tayi , shiyasa anka kaita kotu kuma anka shaidawa alƙali.
Duk Wadannan abubuwa da takeyi babu wanda yake so yaga ƴarsa ko ƙanwarsa tana aikata wadannan abubuwa da take aikatawa, ya saɓa al’umma mu, ya saɓawa addin mu da tarbiyyar mu, wannan sananen abu ne.
Ga cikakken bayani da Sheikh Aminu Daurawa nan yayi ga gidan rediyo.