Majalisar Dattawa ta ƙi amincewa da cire tallafin wutar lantarki
Majalisar dattawan Najeriya ta yi fatali da shirin gwamnatin ƙasar na janye tallafin da take bayarwa a harkokin wutar lantarki, wanda hakan ke nufin kuɗin da ake biya na wutar zai ƙaru.
Majalisar ta dauki wannan matakin ne a zamanta na jiya Laraba.
Sanata Abbas Iya daga Jihar Adamawa ne ya gabatar da ƙudurin wanda ya samu goyon bayan sauran sanatocin da suka halarci zaman na yau.
A tattaunawarsa da BBC Sanata Ali Ndume ya ce babu yadda za a yi a ƙara kuɗin wuta ba tare da sahalewar majalisa ba.
“Wutar da ba ma a samunta ta yaya za a ƙara kuɗinta, a haka ma ni inajin ana karɓar kuɗaɗen da suka wuce iyaka daga hannun alumma”, in ji dan majalisar datawan daga jihar Borno.
Ya ci gaba da cewa a yanzu an fi dogara da wutar sola maimaikon ta Nepa saboda rashin tabbas da kuma tsadarta.
”Don haka babu yadda za mu bari wannan yunƙuri ya tabbata”, in ji sanata Ndume.
Sanatan ya ce dole ne a ƙyale mutane su ji da yanayin da suke ciki na rashin abinci da kuma matsalar tattalin arziki.
~Daily Nigerian Hausa