Labarai

Kishin bil adama :Sojan amerika ya kunna wa kansa wuta akan kisan kiyashi da a ke yi wa falsɗinawa



Akan irin rikici da ake a tsakanin isra’ila da Falasdinawa a gaza wanda ake musu kisan kiyashi wani jami’in tsaro kasar amerika aaron bushnell ya nuna takaicinsa irin yadda abubuwan da ake yiwa mutane gaza bai dace ba yayi zanga-zanga shi kadai kamar yadda wani kwararen marubuci muhsin ibrahim ya ruwaito labarin a shafinsa inda yake cewa.

Sojan sama na Amerika mai suna Aaron Bushnell, ɗan shekera 25, ya kunna wa kansa wuta a gaban ofishin jakadancin Isra’ila (embassy) a Washington DC. Ya yi haka ne don yin Allah wadai da abin da ya kira kisan kiyashi (genocide) da Isra’ila ke yi wa Falasdinawa a Gaza.

Aaron Bushnell
Aaron Bushnell

Aaron ya ta kiran “Free Palestine” bayan ya kunna wa kan shi wutar. Daga ƙarshe dai rai ya yi halinsa a asibiti. Allah Sarki.

 

 

A watan December ma wani ya yi irin wannan a garin Atlanta na Amerika. Ɗauke da tutar Palestine, ya kunna wa kan shi wuta a ƙaramin ofishin hulɗar jakadancin Isra’ila (consulate). Shi dai bai mutu ba.

Babbaka kai (self-immolation) wata hanya ce ta protest tsohuwa a duniya. Idan za ku iya tunawa, an fara Arab Spring, wato tunzirin da Larabawa suka yi a 2010, bayan wani ɗan Tunisiya ya ƙona kansa har lahira.

Allah ya ba mu zaman lafiya, amin.









Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button