Labarai

Kishin ƙasa :Wani babban mutum a Najeriya ya mutu tsabar firgicin za a ci Nigeria

Wani babban Jagora a jam’iyyar APC ya mutu tsabar fargabar za a ci Najeriya a wasan da suka buga da yammacin ranar Laraba, tsakanin Super Eagles na Najeriya da Bafana-Bafana na South Africa,

Mahanga ta ruwaito tsohon Darktan hukumar kula da Neja Delta (NDDC), Cairo Ojougboh ya yanke jiki ya faɗi a ofishinsa dake Abuja bayan da yan wasan Afrika ta Kudu suka samu bugun daga kai sai mai tsaron gida wanda suka ci wasa ya dawo danye a dai-dai ana dab da tashi wasan,

Yan Najeriya da dama sun shiga firgici da bacin rai musamman yadda hakan ya faru ne a dai-dai lokacinda Najeriya ta zura ƙwallo na Biyu a ragar South Africa kafin aka duba na’urar VAR aka iske ashe ɗan wasan Najeriya ya bugi ƙafar ɗan wasan South Africa don haka aka soke sabon cin da Najeriya ta yi sannan aka bayar da P.K ga Bafana-Bafana wanda kuma suka ci.

Tuni dai Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu da sauran Manyan Najeriya da tsohon mataimakin shugaban Ƙasa Atiku Abubakar suka aike da saƙon ta’aziyyarsu ga iyalan mamacin, Cairo Ojougboh

Ojougboh tsohon dan majalisa ne (2003-2007) sannan shine Jagora APC a jihar Delta

A ƙarshe dai yan wasan Najeriya Super Eagles ne suka yi nasara a wasan wanda ya basu damar zuwa matakin karshe wato Final A gasar cin kofin nahiyar Afrika 2023 kuma za su buga da masu masaukin Baƙi wato super Eagles vs Ivory Coast a ranar Lahadi 11 ga watan Fabrairu 2024

Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button