Kannywood

Kalma auri saki da ake alaƙan tani da ita na min ciwo – Adam a zango

Fitaccen jarumin nan a masana’atar Kannywood Adamu Abdullahi zango wanda anka fi kira adam a zango a wannan karo ya samu tattaunawa da wakiliyar BBC Hausa Safiya Dahiru mai shanu a cikin shirin mahangar zamani.

A cikin wannan tattaunawa zaku jarumi adam a zango ya bayyana irin kalubali da ya hada da su sosai duba da irin yadda ya samu sabanin da abokan aikinsa kama da masu shiryawa fina finai furodusas kenan da kuma masu bada umurni daraktas kenan wannan abun ya sanya ya zauce ya shiga wani yanayi da har bayayi abubuwan da sunka dace.

Sai kuma sha’ani na rayuwa shima wannan abu ne da ya shiga wani yanayi na damuwa da baya iya aikata abinda ya dace akansa shiyasa ya hakura kafin ya natsu.

“Mummunar fahimtar da ake min bai fi ba kalma auri saki ba, shi yafin ciwo, bahaushe yakan ce duk wanda maciji ya sara sau daya, to igiya yagani akan hanya sai yaji tsoro, shiyasa wannan abun yasa da nayi na rabu da ita, nayi na rabu da ita , to idan ma na sake hakan ma na iya faruwa da ita.

Kaddara ce ko kana so, ko baka so, ko kana addu’a ko baka addu’a alkawalin Allah baya canzawa, to amma mutane suna da jahilcin fahimtar haka, to shiyasa duk abin nake yi sai ana cewa laifunka ne, to a wannan karo yakamata in gane shin matsalar nawa ne, ko matar da nake aure ko daga gidan da na auro ta ne”.-inji adam a zango

 

Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button