Jima’i na da matuƙar mahimmanci wajen ƙarafawa danƙon soyayya a tsakanin ma’aurata
Jima’i na da matuƙar mahimmanci wajen ƙarafawa danƙon soyayya a tsakanin ma’aurata.
A lokacin saduwa, sinadarin oxyticin da ke taka rawa wajen ƙarfafa dankon alaƙa. Shi dai wannan sinadari na samuwa a lokacin da uwa ke shayar da jaririnta.
Sinadarin Oxytocin, na taimakawa wajen daidaita shaƙuwa, kuma daya ne daga cikin abun da ke karfafa zamnatakewa.
Haka kuma yana taimakawa wajen saurin tsorata, damuwa, da yanayin gajiya; yana samuwa ne a lokacin da aka kusanci juna, a lokacin rungumar juna, ko wasa, ko sumbata.
Hakan na nuni da cewar jima’i bai tsaya da ɓangaren al’aura kaɗai ba, sai dai hanya ce ta samar da daidaito da ke haifar da shaƙuwa.
Duk da cewar inzali shi ne ginshiƙin saduwa ko jima’i, bai kamata alaƙar jima’i ta zama dogaro da wannan sakamakon ba, ko ta gaza cika ba idan har ba a yi nasarar inzali ba.
A taƙaice, jima’i na da alfanu mai yawa. Domin a samu jin daɗi da annashuwa, akwai bukata a bayar da fifiko wajen abin da mutanen da ake jima’in da su ke da buƙata.
Matsa lamba, ko yawaita yin sa, na haifar da gundura. Sirrin shi ne a gano abin da ɗaya ɓangaren yake so, da zai haifar da shakuwa da ƙarfafa alaƙa.
BBC Hausa